1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Iraki

Wani babban jami´in gwamnatin Amirka ya ce shugaba Bush ya damu matuka game da toshiyar baki da sojin Amirka ke ba ´yan jaridun Iraqi don buga wasu rahotanni da suka sabawa ainihin halin da ake ciki a Iraqi. Bush yayi barazanar kawo karshen wannan aiki idan aka tabbatar cewa ya sabawa dokokín aikin jarida. Jami´in ya ce shugaban ya nuna matukar damuwa a saboda haka ya umarci sakataren tsaro Donald Rumsfeld da ya gudanar da bincike akan wannan lamari na biyan kudi don a buga rahotannin da sojin Amirkar ke so a cikin jaridun Iraqi. A yau dai ne a karon farko rundunar sojin Amirka a Iraqi ta amsa cewa ta ba wa kamfanonin buga jaridun kasar toshiyar baki don buga labarai masu dadin ji game da aikin da sojin Amirka ke yi a cikin Iraqin.