Rikicin kasar Iraki | Labarai | DW | 06.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Iraki

Prime minisatn kasar Iraki Nuri Al-Maliki yayi barazanar yanke huldar danganta da kasashen da suka soki zartar da hukunci kisa da akai a akan marigayi Sadam Hussein.Maliki dake zama dan darikar shiyya ya bayyana aiwatar da wannan hukuncin kisa da kasancewa,batu ne cikin gida kuma bai shafi kasashen ketare ba.Ya kara dacewa anyi Sadam ´shariar adalci,kuma zartar da hukuncin kisa da akayi masa nada nufin kawo hadin kai tsakanin yan kasar ta Iraki.Wani hoto na Video da aka dauka da wayar Salula kuma aka yayata,inda ake nuna jamian shia na tozartawa Sadam lokacin rataye shi dai,ya haifar da bacin rai a bangare yan Darikar Sunni ,tare da ruruta kisan gilla a kasar ta Iraki.Adangane da hakane OPrime minister Maliki yace jamian tsaronsa da goyon bayan sojojin Amurka na shirye wajen aiwatar da sabbin matakan tsaroa birnin Bagadaza.