Rikicin kasar Iraki | Labarai | DW | 28.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Iraki

Wasu yan bindiga dadi a birnin Bagadaza sunyi wa babban directa dake maaikatara harkokin masanaantu na kasar Irakin kqwanton bauna ,ayayinda yake tafiya wurin aiki ,inda suka kashe shi da yarsa da wasu jamiansa guda biyu.Rahotan yansanda na nuni dacewa yan bindiga dadin sun rufe motar Adel Abdul Mesun al-Lami ne da harsashin bindigogi a gunduwar Yarmouk dake yammacin Bagadazan.Kakakin maaikatar ya sanar dacewa yarsa Mr Lami da aka kashen ,tana aiki a maaikata masanaantun ne a matsayin Injiniya.Sauran mutane biyu da aka kashe tare dasu kuwa suin hadar da matukin motarsa,da wani jamiin maaikatar da baa gane ba.