Rikicin kasar Iraki | Labarai | DW | 19.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Iraki

Tashin boma bomai da aka dasa su cikin motoci a garin Kirkut mai albarkatun mai dake arewacin Iraki,ya kashe mutane 15,ayayinda wasu sama da wasu 30 suka jikkata.Wadannan boma bomai dai sun tarwatse ne kusan cikin tsukin mintuna ,daga bangarori daban daban na wannan birni na Kirkut.Kazalika a fadar gwamntin kasar ta Iraki dake Bagadaza kuwa ,akalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu ayau,ayayinda wasu 10 suka jikkata,sakamkon hare haren boma bomai.Wadannan hare hare na yau dai sunzo ne adaidai lokacin da Commandan rundunar dakrun Amurka a Iraki General David Petraeus ya sanar ta kafofin yada labaran kasar cewa,an fara samun lafawa ta fannin hare haren da ake kaiwa,tun bayan da karin dakrun Amurka dubu 20 suka fara isa kasar.