Rikicin Kasar Iraki | Labarai | DW | 16.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Kasar Iraki

Akalla mutane 85 ne suka rasa rayukansu yau a Iraki,sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai da wasu manyan motoci guda biyu , agarin Kirkut.Jamian yansanda sun sanar dacewa kimanin mutane 180 ne suka jikkata a awannan harin,tare da sanarwa cewa zaa iya samun karuwan mace mace, awannan birni dake arewacin Bagadazada tuni ake fuskantar rikici,inda kuma ake da kabilun Kurdawa da Turkawa da yan Shia da Sunni da Larabawa.Ana dai shirin gudanar da kuriar raba gardama ,adangane da makomar Kirkut din nan gaba.General Torhan Abdul Rahman na rundunar yansanda,yace anyi asaran gidaje da ginin shaguna, sanadiyyar wannan harin bomb din na yau.