1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Iraki gabanin zaben ´yan majalisar dokoki

December 10, 2005
https://p.dw.com/p/BvH7

An gano gawar wani dan kasar Masar da aka yi garkuwa da shi a Iraqi a yau asabar a daidai lokacin da wa´adin da aka bayar na kisan wasu ´yan kasashen yamma 4 da su ma aka sace su a Iraqin ke karewa. Yanzu dai kasar na cikin wani yanayi na tashe tashen hankula yayin da ya rage kwanaki kalilan gabanin zaben ´yan majalisar dokoki a cikin mako mai zuwa. An gano gawar Mohammed Ibrahim al-Hilali mai shekaru 46 a wani yanki da ke arewa da birnin Tikrit bayan an yi garkuwa da shi da yammacin jiya juma´a. Shi dai al-Hilali yana aikin gina wani asibiti ne a birnin na Tikrit da taimakon kudi daga Amirka. ´Yan tawayen da suka yi garkuwa da ´yan kasar Kanada biyu da Ba-Amirke daya da kuma dan Birtaniya daya sun yi barazanar kashe su idan ba´a biya musu bukatunsu har zuwa yau asabar ba. Har yanzu kuwa ba´a ji duriyar wata Bajamushiya da wani injiyan Faransa da kuma wani Ba-Amirke ma´aikacin tsaro da aka yi garkuwa da su a Iraqin ba.