Rikicin kasar Iraƙi ya dauki sabon salo inda aka kashe sojojin Amirka 7 | Labarai | DW | 23.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Iraƙi ya dauki sabon salo inda aka kashe sojojin Amirka 7

An kashe sojojin Amirka guda 7 a hare haren bam da aka kai a gefen hanya a ciki da wajen Bagadaza babban birnin Iraqi. Mutuwar sun ta zo ne a daidai lokacin da dakarun Amirka da na Iraqi suka shiga kwana na 5 suna kai farmaki akan ´yan al-Qaida a sassa daban daban na kasar. A kuma can lardin Diyala dake arewa maso gabashin Bagadaza, dakarun Amirka da takwarorinsu na Iraqi sun kame kusoshi biyu na kungiyar al-Qaida. To amma laftanan janar Raymond Odierno ya ce daukacin shugabannin al-Qaida sun tsere daga lardin na Diyala gabanin a kai wannan farmaki. Rundunar sojin Amirka ta ce an kashe mayakan al-Qaida har guda 90 tun bayan kaddamar da gagarumin farmakin a Diyala a ranar talata da ta gabata.