1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Iraƙi ya dauki sabon salo inda aka kashe sojojin Amirka 7

June 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuI3

An kashe sojojin Amirka guda 7 a hare haren bam da aka kai a gefen hanya a ciki da wajen Bagadaza babban birnin Iraqi. Mutuwar sun ta zo ne a daidai lokacin da dakarun Amirka da na Iraqi suka shiga kwana na 5 suna kai farmaki akan ´yan al-Qaida a sassa daban daban na kasar. A kuma can lardin Diyala dake arewa maso gabashin Bagadaza, dakarun Amirka da takwarorinsu na Iraqi sun kame kusoshi biyu na kungiyar al-Qaida. To amma laftanan janar Raymond Odierno ya ce daukacin shugabannin al-Qaida sun tsere daga lardin na Diyala gabanin a kai wannan farmaki. Rundunar sojin Amirka ta ce an kashe mayakan al-Qaida har guda 90 tun bayan kaddamar da gagarumin farmakin a Diyala a ranar talata da ta gabata.