1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RIKICIN KASAR HAITI............

ZAINAB AM ABUBAKAR.February 20, 2004
https://p.dw.com/p/Bvll

Kakakin fadar gwamnatin Amurka Scott McClellan
ya fadawa yan jarida cewa ko kadan ,Amurka bata
muradin shugaba Aristide ya sauka daga wannan
mukami nasa.Yace kasashen Amurka ,da wakilan
kasashe 15 dake yankin Caribbean,Canada,faransa
da sauran kasashe na tattauna yadda zaa warware
wannan rikici ne,amma ba batun sauke shugaban
na Haiti ba.sai dai yace dole ne tattaunawar
tasu ta nemi bangarorin biyu daukan wasu
matakai da zai kasance tudun dafawa wajen ganin
cewa an gano bakin zaren warware rikicin
siyasar Haiti.
A karkashin wannan shiri dai,ana bukatar
shugaban na Haiti ya bawa yan adawan wasu
mukamai a gwamnati,ayayinda zai cigaba da
kasancewa akan mukaminsa har zuwa waadinsa na
shekara ta 2006.Ana dai saran gabatar da wannan
tsari wa gwamnatin Haitin ayau,kana jamiaan
Diplomasiyya zasu tabbatar da ganin cewa an
aiwatar dashi ranar Asabar.Stsarin bugu da kari
na bukatar kafa gwamnati mai zaman kanta
akarkashin jagorancin Prime minista,wanda zai
kula da harkokin kasar,kana ayarin yansanda da
suka samu horo na musamman daga kasashen
waje,zasu kula da harkokin tsaro a Haitin.
Sai dai ayayinda yan tawayen ke cigaba da
fatattakan yansanda daga ofisoshinsu ,ayau din
ne kuma yan kasar waje dake da zama a Haitin
suka fara ficewa daga wannan kasa dake cigaba
da fuskantar rikicin siyasa.Ayayinda gwamnatin
Amurka tayi kira da yan kasar dake Haiti dasu
gaggauta ficewa,Limamin christa Gerald St.
Vincent na Virginia cewa yayi,babu yadda Haiti
zata warware wannan rikici da take ciki ba tare
da agajin kasashen waje ba.Ayau din dai sama da
yan Amurka da Canada 100 sukayi jerin gwano a
babban filin saukan jiragen saman kasa da kasa
dake birnin Port-au-prince,akan hanyarsu ta
ficewa daga Haitin.
A hannu guda kuma tun ajiya Alhamis ne yansanda
dake arewacin kasar suka tsere da
rayukansu,ayayinda Babban jamiin kungiyoyin
tawaye Guy Philiphie ,yacesuna shirin kai hari
a Cap-Haitien,babban gari na karshe daya rage a
karkashin gwamnati a yankin arewacin
kasar,ayayinda ake cikin shagulgulan bukin
gargajiya na Kanival daya fara gudana
ayau.Philippe dai ya kasance tsohon babban
jamiin yansan da na shugaba Aristide garin na
Cap-Haitien ,kafin yayi gudun hijira a
shekarata 2000,inda daga baya aka zargeshi da
yunkurin kifar da gwamnatin kasar.
A karkashin tsarin da zaa gabatar dai anasaran
shuga Aristide wanda yayi watsi da batun yin
murabus,ya gabatar da wakilinsa guda,da wakilin
yan tawaye,da jammiin diplomasiyya na
waje,wadanda zasu dauki alhakin nada wakilai
tsakanin 9-15,wadanda kuma sune zasu nada Prime
minista da sabuwar gwamnati a Haiti.Tuni dai
Aristide yayi watsi da batun nada prime
minista,kazalika ana kyautata zaton yan tawayen
ma zasuyi watsi da wannan tsari,domin bukatarsu
shine shugaba Aristide yayi murabus.