Rikicin kasar Faransa na kara yin tsamari | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Faransa na kara yin tsamari

Majalaisar gudanarwar Faransa zata zartar da kudiri wadda zata baiwa hukumomin gundumomi damar kafa dokar talala a yankunan su a kokarin shawo kann tarzomar data ki ta ki cinyewa a kasar. P/M Faransa Dominique de Villepin wanda ya baiyana hakan yace daukar matakin ya zama wajibi bisa laákari da yadda tarzomar take kara yaduwa ya zuwa wasu sassa na kasar. A halin da ake ciki rahotanni sun baiyana cewa tarzomar ta bazu a kalla a garuruwa 300. A ranar litinin masu zanga zangar sun cinna wuta a wata makaranta a birnin Toulouse tare da kona motoci da dama. An ruwaito cewa wani dattijo mai shekaru 61 ya rasu a sakamakon raunin da aka yi masa a yayin tarzomar. P/M Faransa Dominique de Villepin yace zaá kara yawan yan sanda 1,500 akan dakarun yan sanda 8,000 wadanda aka tura domin kwantar da tarzomar, bugu da kari yace gwamnati zata samar da karin kudade domin bunkasa Ilimi tare da koyar da sanaóin hannu ga matasa marasa galihu.