1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kan iyakar tsakanin Habasha da Eritrea

Kwamitin sulhu na MDD ya bi sahun sakatare janar Kofi Annan wajen yin kira ga kasashen Habasha da Eritrea da su nuna halin ya kamata a rikicin kan iyaka da suke yi. Bayan shawarwarin da suka yi a birnin New York wakilan kwamitin sulhu sun ce dole a hana wannan rikici yin muni, to sai dai ba su ba da shawarar irin matakan da ya kamata a dauka bisa wannan manufa ba. Da farko dai jami´an MDD dake kusa da iyaka tsakanin Habasha da Eritrea sun ce kasashen biyu sun fara girke dakarun su akan iyakar, wanda haka ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma. Habasha ta ki amincewa da hukuncin da wata hukuma mai zaman kanta ta yanke game da rikicin kan iyakar.