Rikicin kafa gwamnatin hadaka a yankin Palasdinawa | Labarai | DW | 10.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kafa gwamnatin hadaka a yankin Palasdinawa

Babban jamii na hannun daman shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya bayyana cewa ,akarshen makon nan ne akesaran shuagban Palasdinawan zai sanar da lokacin zabea wannan kasa,a wani jawabi da zai gabatarwa alumomin yankin.Wannan bayani yazo ne,bayan Shugaba Abbas ya sanar dacewa babu alamun cimma tudun dafawa adangane da cimma yarjejeniya da gwamnatin Hamas,na kafa gwamnatin hadin kann kasa.Sai dai Premier Ismail Haniya ,a ziyarar daya kai kasar Iran,yayi gargadin cewa ,gaggauta gudanar da zabe a yankin zai dada haifar da karuwan tashin hankali.Ya kuma zargi shugaba Abbas da kokarin sauke ministocin hamas daga mukamansu ta hanyaar tilas.Gwamnatin yankin palasdinawan dai tayi watsi da kiran da kasashen yammaci sukayi mata ,na runguman Izraela amatsayin yantacciyar kasa tare da kawo karshen ayyukan tarzoma.Sakamakon hakane kungiyar TT da Amurka sudakatar da tallafin da sukewa gwamnatin palasdinun.