Rikicin Jos ya ɗauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 25.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Rikicin Jos ya ɗauki hankalin jaridun Jamus

A kasar Zimbabwe har yau ana fama da matsalar rabon filayen noma

default

'Yan gudun hijira a Jos

Daga cikin batutuwan Afirka da suka samu shiga kannun rahotannin jaridun Jamus a wannan makon har da rikicin addinin da ya addabi garin Jos na Jihar Plateaun Nijeriya. Jaridar Süddeutsche Zeitung, a cikin nata rahhoton nuni tayi da cewar:

"Ko da yake ba wanda ya san tahaƙiƙanin abin da ya haifar da wannan rikici, amma kamar yadda ekbishop Kaigama ya nunar, rikicin baya da wata nasaba da addini, ana dai amfani da addini ne don rura wutar rikice-rikice na ƙabilanci da siyasa. Wannan maganar ta fi shafar matasa, waɗanda akasarinsu zama suke na kashe wando a garin Jos kuma masu hangen wani haske game da makomarsu a sakamakon haka 'yan siyasa kan yi amfani da su don cimma buƙatunsu."

Akwai alamar cimma nasarar kafa wata gwamnati ta farar fula a ƙasar Guinea, inda sojoji suka naɗa wani jami'in hamayya kan muƙamin Piraminista. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi nazarin wannan ci gaba tana mai cewar:

"A bayaninsa na amincewa da naɗin da sojojin suka yi masa Jean-Marie Dore, dake da shekaru 71 da haifuwa nuni yayi da cewar ga alamu dukkan masu faɗa a ƙasar Guinea sun ɗauki azamar kakkaɓe ƙasar daga mummunan hali na koma bayan da ta daɗe tana fama da shi...Sai dai da aka sha famar kai ruwa rana a shawarwari tsakanin Moussa Camara, wanda ke ƙasar Burkina Faso yanzu haka don neman sararawa daga raunin da yake fama da shi da shugaban sojoji janar Sekouba Konte akan naɗa wani piraminista farar fula."

A wannan makon ɗaya daga cikin 'yan ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo dake wasa a nan Jamus ya dawo ƙasar inda yayi bayanin abin da ya wakana a Cabinda lokacin da aka kai musu hari. Jaridar Kölnische Rundschau ta ambace shi yana mai ƙarin bayani da cewar:

"Sa'armu ita ce kasancewar sojoji na mana rakiya. Wannan shi ne kawai ya taimaka muka hau tudun na tsira. Dukkanmu mun kaɗu da abin da ya faru, inda aka halaka kakakin ƙungiyar da mataimakin mai koyar da 'yan wasa. Sai dai kuma bayan da muka tattauna mu ya mu, mun tsayar da shawarar shiga gasar. Amma shugaban ƙasa ya dakatarmu. Daga baya dai mun yi baƙin cikin hakan saboda rashin samun wata dama ta nuna ƙwarewarmu, in ji Assimiou Toure ɗan ƙasar Togo dake wa ƙungiyar Bayer Leverkusen wasa a nan Jamus."

Afirka ta Kudu na daɗa ƙara matsin lamba akan Zimbabwe domin ta ƙara yin hoɓɓasa a matakanta na garambawul, kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta rawaito da kuma ci gaba da cewar:

"Maganar rabon ƙasa na daga cikin manyan matsalolin da ake fama da saɓani kansu a gwamnatin haɗin kan ƙasa ta Zimbabwe, kuma kawo yanzu babu wata takamaimiyar alamar dake nuna samun canji bisa manufa. Zimbabwe na buƙatar kuɗi, amma kuma da ƙyar ne take samun rancen kuɗi daga ƙetare. Afirka ta Kudu dai tayi mata alƙawarin taimako a yayinda ita kuma Australiya ta ce zata sake kama matakanta na taimako ga ƙasar. Amma a ɗaya ɓangaren har yau Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce ba zata soke takunkumin da ta ƙaƙaba ba sakamakon tafiyar hawainiyar da ake samu ga matakan garambawul ga manufofin ƙasar ta Zimbabwe."