Rikicin Jamus da Kongo | Siyasa | DW | 21.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Jamus da Kongo

Ana faman kai ruwa rana dangane da buƙatar da wani ɗan kasuwa ya gabatar ta neman kuɗi dala dubu 300 daga hukumar GTZ ta Jamus

default

Aikin sassaƙen katako a Kongo

Wani abin mamaki da ya faru baya-bayan nan a janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo shi ne wani ɗan kasuwar katako ya haɗa kai da wani alƙali domin ɗaukaka ƙara kan hukumar taimakon raya ƙasashe masu tasowa ta Jamus GTZ akan wasu dalilai da ba su da tushe. Alƙalin ya nema daga hukumar ta GTZ da ta biya tarar kuɗi na dalar Amirka dubu ɗari uku kuma a saboda hukumar ta ƙi amincewa da wannan hkunci sai aka ɗora hannu kan ajiyarta a bankunan ƙasar. Wannan maganar na barazanar taɓarɓara dangantaka tsakanin Jamus da ƙasar Kongo dake ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samun taimakon raya ƙasa daga Jamus.

Salula Nour tayi kimkanin shekaru 16 tana gudanar da aikinta a Janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo, inda daga baya-bayan nan take jagorantar ofishin hukumar taimakon raya ƙasa ta Jamus GTZ a Kinshasa. Tun da take kuwa ba ta taɓa tunanin fuskantar wata matsala irin shigen ta baya-bayan nan tare da Tabura Kashali ba. Shi dai Kashali ɗan kasuwar katako ne a garin Goma dake gabacin Kongo, wanda tun misalin shekaru 16 da suka wuce hukumar GTZ ta ba shi kwangilar samar da katako don tafiyar da wani shirin taimakon gaggawa.

"Bayan cimma wajewa akan cinikin a kashe gari GTZ ta tura manyan motoci domin su yi lodin katakon da aka daidaita akansu. Amma ba a samu katako ko da ƙwaya ɗaya a gun ba. A saboda haka GTZ ta ce ba zata biya kuɗin ba. Shi kuma ya dage akan cewar faufau ba zai yarda ba, wai saboda ya ajiye katakon a nan wurin, sacewa aka yi. A saboda haka dole ne mu ba shi kuɗin saboda ya biya masu sayar masa da katako."

Ɗan kasuwar yayi bakin ƙoƙarinsa tare da gabatar da ƙararraki daban-daban har sai da ya kai maganar gaban kotun Ƙoli ta ƙasar Kongo, wadda ta sa ƙafa tayi fatali da ƙararsa, kuma gwamnati ta biya shi diyyar asarar da ya ce yayi. Amma Kashali bai dadara ba yana mai sake gabatar da ƙara gaban wata 'yar ƙaramar kotu, lamarin da tsarin dokar ƙasar bai amince da shi ba. Sai dai ga alamu yayi wa alƙalin kotun alƙawarin ba shi wani kaso na kuɗin ya kuma nemi ƙarin riba ta dalar Amirka dubu metan da hamsin. Rene Ngongo, mai fafutukar kare kewayen ɗan-Adam yayi kakkausan suka akan tsarin dokar ƙasar Kongo inda ya ce:

"Wannan abin mamaki ne kasancewar an ɗora hannu akan kuɗeɗen saboda wannan hukunci maras ma'ana. Ita GTZ ta kawo mana taimako a lokacin da muke fama da yaƙi a yayinda sauran ƙungiyoyin taimako suka tattara nasu ya nasu suka yi gaba. Idan mutum ya manta da wannan karimci, to kuwa hakan ba zai zama barazana ce ga alaƙa da Jamus kaɗai ba har ma da sauran ƙasashe, waɗanda zasu ɗauki abin tamkar cin mutunci."

Shi ma dai ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya bayyana fushinsa matuƙa ainun da wannan halin da aka shiga. Domin kuwa ba ɗan kasuwar katakon ne kawai ke neman yin amfani da wannan dama don ci da gumin GTZ ba, har ma da wata ƙungiyar taimako ta ƙasar Kongo dake zaman kanta, wadda a sakamakon dakatar da ma'amalla da ita da GTZ tayi take neman diyyar dala miliyan ɗaya daha hukumar. Dirk Niebel ya ƙara da bayanin cewar:

"Wannan ba abin karɓuwa ba ne. Babban alhakin dake kanmu shi ne mu tabbatar da cewar ba a yi ɓarna da kuɗaɗen haraji daga Jamus ba. Ba zata yiwu su kwarara zuwa aljihun wani ɗan kasuwar katako ba, sai dai a yi amfani da su a shirye-shiryen kyautata rayuwar al'umar Kongo da raya makomar yankin baki ɗaya."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu