1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC a Najeriya na fama da rikici

May 10, 2018

A wani abun da ke zaman alamun rikicin da ke tafe cikin jam’iyyar APC mai mulki, wasu jiga-jigan jam'iyyar sun ce sun bai wa gwamnati tsawon mako guda domin sake taku da kuma gyara ko kuma su fice su kama gabansu.

https://p.dw.com/p/2xVDW
Karikatur: Nigeria APC Streit
Rikicin cikin gida ya addabi jam'iyyar APC mai mulki a NajeriyaHoto: DW / Abdulkareem Baba Aminu

Tuni dai wata wasikar tsofaffin 'ya'yan jam'iyyar PDP da suka taka rawa wajen kafa jam'iyyar APC da ma taimaka mata cin zabe, ke neman tayar da hankali na masu tsintsiyar da ke neman hanyar mikewa a cikin mulki na kasar. Karkashin jagorancin Kawu Baraje dai, manyan jiga-jigan jam'iyyar sun shaidawa masu jarida a shelkwatar jam'iyyar da ke a Abuja, cewar tura fa ta kai bango kuma an kare hakurinsu. Rikicin cikin gidan APC dai na daukar launin tsumangiyar kan hanya fyade yaro fyade babba. Ko bayan 'yan sabuwar PDP da ke korafin yi basu dai, suma magoya baya na  shugaban kasar na kallon an saba a cikin tsarin da ke gudana a ajihohi yanzu a fadar Solomong Dalung da ke zaman jigon APC kuma minista a gwamnatin ta Buhari.

Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

Kalubale yayin da zabe ke tafe

Adalci a tsakani na masu tsintsiya ko kuma tofin alatsine a cikin hallayar manya dai, daga dukkan alamu jam'iyyar APC na shirin gani na ba zata da ma kila babban rikici a cikin gwagwarmaya ta neman tasiri da kila ma mulki a matakai daban-daban. Auwal Mu'azu dai na sharhi kan lamura na siyasa ta kasar kuma a fadarsa abin da ke faruwa a halin yanzun, na zaman aiken sako na irin hanyar da  APC take shirin ta bi. Abun jira a gani dai na zaman tasirin rigingimun cikin gidan na APC da ke kara kusantar zabe amma kuma ke kallon rikici ta ko'ina.