Rikicin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango | Labarai | DW | 29.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango

Rikicin siyasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango na ci gaba da yin kamari, bayan da masu ruwa da tsaki kan al'amuran da suka shafi al'umma da ke kokarin shawo kansa suka fara tsame hannunwansu.

Shugaban Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango Joseph Kabila

Shugaban Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango Joseph Kabila

Guda daga cikin irin wadannan muhimman mutane da suka tsame hannunwa nasu dai, shi ne Archbishop Marcel Utembi wanda ke zaman mai shiga tsakani a rikicin da ya ce ya cire hannu a kan batun sulhun. Matakin na Archbishop Utembi dai baya rasa nasaba da abin da aka bayyana da rashin gaskiya daga bangaren manyan 'yan siyasar kasar. Rikicin na Kwango dai na kara ta'azzara bayan da jam'iyyun da ke cikin gwamnatin hadaka suka ki amincewa a nada Firaminstan rikon kwarya daga bangaren 'yan adawa, wanda zai rike ragamar mulkin kasar gabanin zabe. Tun dai da aka dage babban zaben kasar tare da kara wa'acdin mulkin Shugaba Joseph Kabila wanda wa'adin mulkin nasa ya cika ba tare da gudanar da zabe ba, kasar ta Kwango ta tsunduma cikin rikici.