1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Isra´ila da Palestinu

Yahouza Sadissou MadobiSeptember 6, 2006

Rundunar Isra´ila na ci gaba da kai hare -hare a yankunan Palestinawa

https://p.dw.com/p/BtyL
Hoto: AP

Daga wayewar sahiyar wanan laraba, zuwa yanzu a ƙala mutane 7, su ka rasa rayuka a zirin Gaza, a sakamakon hare-haren Isra´ila.

Rahotanin daga yankin sun ambata cewar, a ƙalla motoci masu sulke 10, tare da jiragen sama masu durran angulu, su ka kai samame, tare da capke mutane da dama.

Isra´ila na zargin su, da masaniya a game da maɓuyar Galid Shalit,sojan ta ɗaya, da yan ƙungiyar Hamas ke garkuwa da shi.

Mutanen da su ka rasu, sun haɗa da Mujahid Al-Saleh shugaban reshen ƙungiyar Jihadil Islami ta birnin Jenine, da Isra´ila ke nema ruwa jallo.

Tun ranar 24 ga watan juni da ya gabata Isra´ila ta matsa ƙaimi, ga farautar yan ,kungiyar yaƙin sunƙuru da ta ke zargi da kame Gilad Shalit.

Daga wannan lokaci zuwa yau, fiye da mutane 200 su ka kawnta dama, a sanadiyar ruwan bama baman Isra´ila.

Bayan kashe kashen, Isra´ila ,ta kame shugaban Majalisar Dokokin Palestinu Aziz Doweik da yan majalisu da kuma ministoci kussan 30 a matsayin matakin maida martani.

Shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da bada tallafi ga yan gudun hijira, John Ging, ya ce al´ummomin zirin Gaza, na fama cikin uƙuba, a game da haka, yauni ya rataya, a kan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, su duba wannan matsali da idon rahama.

Shugabar hukumar bada agaji a yanukan da Isra´ila ta mamaye, Maskit Bendel, da ke gane wa idon ta yau da kullum, mayuhacin hali da Palestinawa ke ciki, ta hurta cewa :

„A lokacin yaƙi da Libanon Isra´ila, ta cigaba da yin ruwan bama bamai a zirin Gaza, abunda ya ƙara saka mazauna yankin cikin hali uƙuba, mussamman ma, tun bayan kame Galid Shalit sojan nan na Isra´ila.

Duk da tallafin kuɗaɗen da aka ambata baiwa hukumar palestinawa, ba ni tunanin za a samu cenji ta fannin kyautata rayuwar jama´ar yankin.

A dangane da mattakan kawo ƙarshen wannan rikicin jami´ar ta ci gaba da cewa:

„Na farko dai, mu na bukatar ganin an azza tubalin tushe, na kawo ƙarshen mamayen yankunan Palestinawa.

Mu na so, a dasa aya, ga dukan hare haren da ake kaiwa, sannan a buɗa hanyoyin zirga zirga.

Mataki na gaba ko shaka babu, shine na zama tebrin shawarwari tsakanin hukumar palestinu, da gwamnatin Isra´ila.

Wannan itace hanyar da mu ke sa ran, zata iya cenza yanayin da ake ciki yanzu.“

A ɓangaren diplomatia , ƙungiyar gamaya turai, ta bakin minsitan harakokin wajen Finlande, da ƙasar sa, ke jagorantar EU, tayi kira ga gwamnatin Isra´ila, ta yi belin yan majalisun dokoki, da minsitocin Palestinu da ta kame.

Kazalika ranar assabar mai zuwa idan Allah ya kai mu, za agana tsakanin Praministan Britania Tony Blair, da tkwaran sa Ehud Olmert na Isra´ila, inda za su tantana rikicin gabas ta tsakiya.