Rikicin Isra´ila da mayakan Hisbollah | Labarai | DW | 10.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Isra´ila da mayakan Hisbollah

Sojojin Israila suna cigaba da gwabza yaki da dakarun Hizbollah a yayin da suke kara matsowa zuwa garin Khiam dake kudancin Lebanon. Daman jiragen yakin Israila sun kara kaimi wajen yiwa garin amman wuta. Kuma tuni sojojin Israila suka shiga biranen Mar-jaun da Qla-iah inda masu biyan addinin kirista suka fi karfi. Ko da yake jami’an yakin Israila sun ce hare haren kadan ne daga farmakin da aka yarda musu wajen taron kasar a jiya laraba. A halin yanzu dai, dakarun Hizbollah sun cigaba da harba rokoki a arewacin Israila. Jami’an kiwon lafiya sunce mutane biyu da wani dan jariri sunka rasa rayukan su a hare haren.