1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Isra´ila da Hezbollah

August 8, 2006
https://p.dw.com/p/BunQ

A na ci gaba da ɓarin wuta tsakanin dakarun Isra´ila da na Hezbollah a kudancin Labanon.

Bayan taron da su ka gudanar jiya, a birnin Beyruth ministoci harakokin wajen ƙasashen larabawa sun nuna goyan baya, ga gwamnatin Labanon a dangane da shawara da ta bada ta hita daga wannan rikici.

ƙasashen na larabawa sun nuna adawa da ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Dunia ke shirin ɗauka, na samun tsagaita wuta.

Ministocin harakokin wajen ƙasashen larabawa sun tura tawaga zuwa birnin New York, na ƙasar Amurika, inda za su halartar taron komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Jikadan France a Majalisar DE la Sabliere, ya ce komitin a shire ya ke,, ya sake duba wannan ƙudduri, da France da kuma Amurika su ka gabatar wa Majalisar.