Rikicin Isra´ila da dakarun Hisbollah a birnin Bint Jubeil | Labarai | DW | 26.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Isra´ila da dakarun Hisbollah a birnin Bint Jubeil

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya nunar da cewa alhakin yin sulhu mai dorewa ya rata a wuyan kasashen wannan yanki ciki har da Syria da Iran. Shi kuwa ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya bayyana taron na Libanon da cewa yayi nasara. Ministan ya ce yanzu an kawad da sabanin ra´ayi da aka samu bayan barkewar wannan rikici. Duk da taron na birnin Rome, har yanzu ana ci-gaba da gwabza wani mummunan gumurzu tsakanin dakarun Hisbollah da sojojin Isra´ila don karbar ikon garin Bint Jubail dake kudancin Libanon, wanda ya kasance cibiyar Hisbollah. Wata tashar telebijin Larabawa ta rawaito cewa an kashe sojin Isra´ila 13 sannan aka yiwa 25 rauni, to amma rundunar sojin Isra´ila ba ta tabbatar da haka ba. Hisbollah ta lashi takobin ci-gaba da yakin sunkuru tare da harba rokoki cikin Isra´ila, inda a yau din nan ma ta harba rokoki da dama zuwa birnin Haifa. Shugaban Hisbollah Hassan Nasrallah ya ce in ban da yakin na Bint Jubeil Isra´ila ba zata kai labari ba.