1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Amirka da Turai sun jaddada kudirin aiki tare

Suleiman BabayoApril 25, 2016

Shugaba Barack Obama na kasar Amirka ya yi wata ganawa ta musamman da shugabannin manyan kasashen Turai masu karfin tattalin arziki, yayin ziyarar aiki da yake yi a kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/1IcSS
Hannover Gespräch Staatspräsidenten Obama Renzi Hollande mit Bundeskanzlerin Merkel vor Beginn US-Europa Gipfeltreffen
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Shugabannin daga kasashe mafiya karfin tattalin arziki na Turai sun hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da Firaminista David Cameron na Birtaniya, da Shugaba Francois Hollande na Faransa, gami da Firaminista Matteo Renzi na Italiya, kuma maganar dakile tsagerun kungiyar IS mai ikirarin kafa daular Islama ta mamaye tattaunawar. Wannan batu ya mamaye daukacin tattaunawar da Shugaba Obama na Amirka ya yi da shugabannin kasashen da ya ziyarta da suka hada da Birtaniya da Saudiyya.

Deutschland Merkel, Obama, Hollande, Renzi und Cameron in Herrenhausen
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Obama ya yi alkawarin kara tura tura sojojin musamman 250 wadanda za su taimaki 'yan tawayen Siriya kan yaki da 'yan kungiyar IS. Tun farko shugaban ya nuna muhimmancin aiki tare da wajen dakile irin hare-haren da aka samu a kasashen Faransa da Beljiyam da ke Turai, gami da taimakon Siriya da Iraki magance matsalolin tsageru.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta karfafa wannan magana amma ta nuna damuwa ganin cewa ana zaman sasantawa tsakanin bangarorin da ke rikici a Siriya, sannan kuma ana karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Deutschland Merkel, Obama, Hollande, Renzi und Cameron in Herrenhausen
Hoto: Reuters/G. Bergmann/Bundesregierung

A daya hannun Shugaba Barack Obama na kasar Amirka ya kuma nuna muhimmancin amfani da hanyoyin sulhu wajen kawo karshen rikici Siriya da ya haifar da 'yan gudun hijira:

Ita dai kasar Siriya ta tsunduma cikin yakin basasa a shekara ta 2011 yayin boren neman kawo karshen gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.