RIKICIN IRAKI DA IRAN DA SYRIA KAN YAN TAADDA. | Siyasa | DW | 16.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RIKICIN IRAKI DA IRAN DA SYRIA KAN YAN TAADDA.

Rikicin Taaddanci tsakanin Irak,Iran da Syria.

Rikicin Taaddanci tsakanin Irak,Iran da Syria.

Ministan tsaro na kasar Iraki ya zargi makwabciyarsu Iran da Syria da kasancewa Ummul abaisin karuwan tashe tashen hankula a wannan kasa saboda tallafi dasuke bawa Abu Musab al zarqawi ,da tsoffin mukarraban tsohon shuagaban Iraki Sadam Hussein.

Hazim al-Shaalan yayi wanna zargin ne ayayinda yake jawabi wa dakarun Amurka,Britania ,da Iraki da wasu jamian tsaro dake wannan kasa.Ministan tsaron ya jaddada cewa Iran nada sansanain yan tarzoma data girke acikin kasar ta iraki.Prime ministan Iyad Alawi dai yasha zargin kasar ta Iran da hannu dumu dumu cikin irin tashe tashen hankula da Irakin ke cigaba da kasancewa ciki tun bayan kifar da gwamnatin Sadam hussein zuwa yanzu da ake shirin gudanar da zaben kasa baki daya.

Shaalan yace Iran da Syria na masu kasancewa makiyan Iraki,domin suna taimakawa kungiyar Musab al-Zarqawi,kungiyar da take cigaba da daukan rayukan mutanaen Irakin ta hanyar dasa boma bomai dakai hare hare,tare da sace yan kasashen waje dake aiki a Irakin.

Ya bayyana cewa yanzu haka kasarsa na muradin kasancewa kann tafarkin democradiyya ,ayayinda makwabtan nasu ke son su cigaba da zama cikin kunci da mulkin Danniya .

Shi kuwa Shugaban Amurka George W Bush gargadi yayi wa Iran da Syria dasu tsame hannunsu daga harkokin Iraki.Tuni dai Iraki da Syria suka karyata wannan zargi da ake musu na wata halaka da kungiyoyin yan tadda dake kasar ta Iraki.A dangane da hakane dayake mayar da martani dangane da jawaban ministan tsaron Irakin,ministan harkokin cikin gida na Iran Abdolvahed Mousavi-Lari ya fadawa yan jarida cewa ,Shaalam bashi da abun fadi ne kawi shi yasa yake wannan zargin da bashi da tushe.Yace yasan kalaman nasa umurni daga ubbanin gidansa

Iran da Irakin dai sun jima da kasancewa cikin sabani tun basyan da dakarun Sadam suka mamaye Iran a shekarata 1980,bayan juyin juya halin kasar ,wanda ya jagoranci yaki tsakanin kasashen biyu na tsawon shekaru 8.

Ayayinda yawancin Larabawan yan darikar Sunni ne ,kashi 60 daga cikin 100 na yan Iraki yan darikar Shia ne,kamar yawancin yan Iran din.

Zainab A Mohammed.