1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rikicin Horar da jami'an tsaro a Libya

Cigaban mahawara dangane da irin rawa da gwamnatin Jamus ta taka a horar da jami'an tsaron

default

Muammar el Gaddafi,shugaban Libya.

Ana ci gaba da fama da kai ruwa rana dangane da tabargazar ba da horo ga jami'an tsaron Libiya da wasu ‘yan sandan Jamus suka yi a asurce. An dai fallasa abubuwa da dama, amma ba a da wata tabbatacciyar shaida a game da masu hannu a wannan tabargaza, sai dai kawai lalube ake yi a cikin duhu.

A cikin wani rahoton da ta gabatar a jiya lahadi jaridar nan mai suna Bild am Sonntag ta yi ikirarin cewar tsofon shugaban gwamnati Gerhard Schröder shi ne yayi wa shugaban juyin-juya-halin Libiya Mu'ammar Gaddafi alkawarin taimakawa wajen bai wa jami'an tsaronsa horo lokacin wata ganawar da suka yi a shekara ta 2004. Dalilin wannan alkawarin kuwa shi ne domin bayyana godiyarsa da irin rawar da Libiya ta taka wajen sakin wasu Jamusawan da aka yi garkuwa da su a kasar Philippines a shekara ta 2000. Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta rawaito cewar ma'aikatar tsaron Jamus na da hannu dumu-dumu a wannan tabargaza, inda ta ce a tsakanin shekara ta 2005 da ta 2006 shugaban rukunin masu tsaron lafiyar manyan jami'ai na sojan Jamus Wolfgang Schneiderhan ya ba da horo ga masu tsaron lafiyar shugaba Gaddafi. Amma ma'aikatar tsaro ta dakatar da bincike akan maganar a wajejen tsakiyar shekara ta 2006.

Rahotanni na farko-farko da aka samu sun yi ikirari ne cewar ‘yan sanda daga jihar Northrhine-Westfaliya da ake zarginsu da wannan laifi, kwangila suka samu daga wani kamfani mai zaman kansa ba tare da sanin mahukunta ba. Sun amince da kwangilar ne akan ba wa jami'an tsaron Libiya horo lokacin da suke hutu. Mahukunta masu daukaka kara a birnin Düsseldorf sun gabatar da matakai na bincike akan lamarin kamar yadda wani mai magana da yawunsu ya nunar ya kuma kara da cewar:

“Kawo yanzun dai babu wata shaidar dake tabbatar mana da cewar hukumar leken asirin Jamus na da hannu a lamarin. Kazalika babu wasu cikakkun bayanan dake tabbatar da ikirarin da ake yi na cewar an gudanar da shawarwarin ba da horo ne a ofishin jakadancin Jamus dake Tripoli.”

Rahotanni masu nasaba da kafofin yada labarai sun yi ikirarin cewar hukumar leken asirin Jamus na da cikakkiyar masaniya game da abubuwan dake faruwa. Amma wani mai magana da yawun hukumar ya musunta hakan. Ita ma mujallar nan ta Der Spiegel sai da ta rawaito cewar ofishin jakadancin Jamus dake Tripoli na labarin wannan hadin kai da aka ba wa Libiya. A halin da ake ciki Wolfgang Bosbach, kakakin jam'iyyar CDU a majalisar dokoki ya ce wajibi ne a gudanar da bincike, inda ya kara da cewar:

“Zan yi mamaki matuka da aniya idan har za a gano cewar hukumar leken asiri ta Jamus ko kuma ofishin jakadancin kasar a Tripoli su ne suka amince da hakan.”

Dukkan jam'iyyun siyasar dake da wakilci a majalisar dokoki sun nema daga kwamitin bincike na majalisar da yayi zama na musamman akan wannan tabargaza. Kuma ga alamu a jibi laraba idan Allah Ya kaimu, ita kanta majalisar dokoki ta Bundestag zata tattauna wannan batu.