Rikicin hayakin gas a tsakanin Russia da Ukraine | Labarai | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin hayakin gas a tsakanin Russia da Ukraine

A yayin da rikicin hayakis gas a tsakanin kasar Russia da Ukraine ke kara daukar sabon salo, ministan tattalin arziki na Jamus, wato Michael Glos yace wannan rikici ba zai shafi katsewar hayakin gas din daga Russia izuwa Jamus ba.

Ministan , wanda ya fadi hakan yayin da yake zantawa da yan jaridu, ya kara da cewa a yanzu haka Jamus nada ajiyayyen hayakin gas din da zai ishe ta izuwa wani lokaci koda za a samu matsala game da aiko da hayakin gas din daga Russia izuwa Jamus.

Ba a da bayan haka, Michael Glos ya kuma tabbatar da cewa akwai kuma wasu hanyoyi da kasar zata bi don cike gibin katsewar hayakin gas din daga kasar ta Russia .

Rahotanni dai sun nunar da cewa kashi 35 daga cikin hayakin gas din da Jamus take amfani dashi, tana sayen sane daga kasar ta Russia.

A karshe Michael Glos yayi amfani da wannan dama wajen kiran kasashen biyu dasu koma teburin sulhu don warware wannan takaddama dake tsakanin su.

Wannan dai rikici a tsakanin kasashen biyu ya samo asali ne bayan da mahukuntan na Russia suka ce zasu kara farashin hayakin gas din ga kasar Ukraine, wanda kuma tuni mahukuntan na Ukraine sukayi watsi da wannan aniya, inda a yanzu ta kai ga katse hayakin gas din da kasar ta Russia take sayarwa kasar ta Ukraine.