1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Hamas da Fatah

dakarun Hamas da na Fatah, masu yaƙar juna da su tsagaita wuta.

Duk da yarjejeniyar sulhu da ƙungiyoyin 2 su ka cimma, sun ci gaba da barin wuta ranar jiya asabar, inda a ka kiyastewar mutane a kala 10 su ka ji raunuka.

Ko da shike dai, rikicin bai yi munin na kwanakin da su ka gabata ba, amma wani mataki ne,na maida hannun agogo baya, ga yarjejeniyar sulhun.

Itama Iran, da ke matsayin ɗaya, daga ƙasashe masu faɗa aji a yankin gabas ta tsakiya, ta yi kira ga Hamas da Fatah su ajje makamai, su kuma girka gwamnatin haɗin ƙasa, wanda a cewar hukumomin Teheran, ita ce hanya ɗaya tilo da za ta kai ga cimma nasara.

Bisa dukan alamu, ƙungiyoyin Palestinu sun ji wannan kira, sun kuma amince da janye dakarun su daga titina, a sakamakon wata sabuwar yarjejniyar da su ka rattaba wa hannu, a yammacin jiya asabar.