Rikicin Gwajin Makaman nuklear Korea ta Arewa | Labarai | DW | 10.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Gwajin Makaman nuklear Korea ta Arewa

Ƙasashen dunia na ci gaba da hurta ra´ayoyi, a game da gwajin makaman nukleya, da Korea ta Arewa ta yi, ranar litinin da ta gabata.

Ƙasashen masu kujerun didindin a komitin sulhu an Majalisar Ɗinkin Dunia, a karo na farko, sun ɗauki matakin bai ɗaya na yin Allah wadai, ga Korea ta Arewa. Sannan sun amince da tantanawa, akan batun hukunta wannan ƙasa.

Nan gaba a yau ne, a ka tsara komawa tantanawa,domin tunani a kan shawarwarin da Amurika da Japon ,su ka bada, na hukuncin da ya kamata, a ɗauka, a kan Hukumominn Pyong Yang.

Hata da Sin, da ke sahun gaba, daga ƙasashe masu goyan bayan Korea ta Arewa, ta nuna ɓacin rai ga wannan gwaji, kamar yadda Wang Guangya, jikadan Sin, a Majalisar Dinkin Dunia, ya bayyana.

A nasa ɓanagaren, ministan harakokin wajen Jamus, Franck Walter Steinemeir, yayi kira ga Korea ta Arewa ta koma tebrin shawawari, ba da ɓata lokaci ba, domin warware wannan rikici cikin ruwan sanhi.

Mallakar makamain nuklea ga ƙasar , ba ƙaramin haɗarin ba ne, ga zaman lahia a yankin inji Steinmeir.

A halin da ake ciki dai, Amurika ta shiga bincike, domin haƙiƙance gaskiyar gwajin makaman nuklear, na Korea ta Arewa.