Rikicin gwajin makaman nukiliyar Koriya Ta Arewa | Labarai | DW | 07.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin gwajin makaman nukiliyar Koriya Ta Arewa

A yau asabar KTA ta sake yin kira ga Amirka da ta janye dakarunta daga KTK. Yanzu haka dai Amirka ta girke dakaru kimanin dubu 30 a kasar ta KTK. Wannan kiran ya zo ne bayan da kasashe membobin kwamitin sulhun MDD suka amince da wata sanarwar hadin guiwa wadda ta yi kira ga KTA da ta yi watsi da shirin ta na yin gwajin makaman nukiliya na farko a cikin kasar. Hakazalika an kuma yi kira gareta da ta koma kan teburin shawarwarin nan na kasashe 6 game da dakatar da shirinta na nukiliya. Jami´an gwamnatin Japan sun ce sun yi imani KTA ka iya yin gwajin a karshen wannan mako. A nata bangaren KTA ta ce gwajin na da muhimmanci don dakile abin da ta kira wata barazana ta soji da tattalin arziki daga Amirka.