1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin gwajin makamai na Koriya Ta Arewa

July 7, 2006
https://p.dw.com/p/BurI
Duk da sukar da take sha daga ko-ina cikin duniya kasar KTA ta ce zata gudanar da sabbin gwaje gwajen makamai masu linzami. Kamfanin dillancin labarun KTK ya rawaito wata sanarwa daga ma´aikatar harkokin wajen KTA na cewa dakarun kasar zasu ci-gaba da gwajin makamai masu linzami da suka fara a tsakiyar wannan mako. Sanarwar ta ce gwajin wani bangaren ne na atisayen soji wanda KTA ta bayyana da cewa yana cikin wani shiri na fadada harkokin tsaron ta. Gwamnatin birni Pyongyang ta yi barazanar mayar da martani idan kwamitin sulhun MDD ya goyawa Amirka da Japan baya aka kakaba mata takunkumi. Kasashen Rasha da Sin sun na saka ayar tambaya game da daukar wannan mataki. Ko da yake gamaiyar kasa da kasa ta fusata game da gwaje-gwajen amma ra´ayi ya bambamta akan martanin da aka mayar.