1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270109 Dialog Gazakrieg AJMF

Mohammad AwalJanuary 30, 2009

Rikicin da ake yi a Zirin Gaza tsakanin Isra´ila da Ƙungiyar Falasɗinawan Hamas ya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin ´ya´yan ƙungiyar abokantaka ta Yahudawa da Musulmi a ƙasar Faransa wato AJMF.

https://p.dw.com/p/Gjlo
Hoto: AP

Rikicin da ake yi a Zirin Gaza tsakanin Isra´ila da Ƙungiyar Falasɗinawan Hamas ya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin ´ya´yan ƙungiyar abokantaka ta Yahudawa da Musulmi a ƙasar Faransa wato AJMF. A halin da ake ciki wakilan Musulmai sun fice daga wannan ƙungiya. To komene ne dalili? Za ku ji ƙarin bayani.

Kimanin Musulmai miliyan biyar da Yahudawa dubu 600 ke zaune a Faransa, wato adadi mafi yawa na biya waɗannan addinai biyu idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Turai. A kwanakin nan gwamnati a birnin Paris ta nuna damuwa cewa rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya ka iya janyo saɓani tsakanin addinai a ƙasar. Yanzu dai an fara ganin tasirinsa, domin rikicin na Zirin Gaza ya haddasa rarrabuwar kawuna a cikin ƙungiyar abokantaka ta Yahudawa da Musulmai wato AJMF a Faransa, inda shugabannin Musulmai suka ajiye muƙamansu.

Wannan ƙungiya ta abokantaka tsakanin Yahudawa da Musulman Faransa, tana da shugabanni biyu wato Bayahude da kuma Musulmi. To amma tun a tsakiyar wannan wata na Janeru, limamin Yahudawa Rabbi Michel Serfati ne kaɗai ke shugabantar ƙungiyar. Takwaransa Musulmi a kujerar shugabancin wato Jelloul Seddik wanda har wayau shi ne daraktan cibiyar nazarin addini ta manyan masallatai a Paris, ya yi murabus. A cikin wata sanarwa da ya bayar Seddik ya ba da dalilin yin murabus ɗin na sa da cewa takwaransa Bayahuden ya ƙi fitowa fili ya bayyana matsayinsa danagne da abin da ya kira laifukan yaƙi a Zirin Gaza. To sai dai Rabbi Serfati ya kare kansa yana mai cewa.

“A rana ta biyu na wannan rikici tsakanin Isra´ila da Hamas Jalloul ya buga mun waya inda ya gaya mun cewa hankalin mutane ya tashi sosai a masallacin juma´ar birnin Paris. Ya kuma ƙara da cewa da shi da shugaban masallacin wato Dalil Bubakar za su iya kwantar da hankulan mutane sannan shi kan shi shugaban masallacin zai ba da wata sanarwa tsakani da Allah game da rikicin na Gaza. Ya ce ya kamata mu yi biyayya ga dokokin ƙungiyarmu kana kuma mu nesanta kanmu daga batutuwan siyasa musamman waɗanda suka shafi rikici tsakanin Isra´ila da Falasɗinawa. Ya roƙe ni da in yi shiru kuma ka da in yi wani abu dangane da wannan batu.”

Limamin na Yahudawa ya ƙara da cewa wannan ita ce hirarsu ta ƙarshe da takwaran na sa. Ya ce ta kafofin yaɗa labarai ya samu labarin murabus ɗin sa. Kuma duk ƙoƙarin da Rabbi ɗin ya yi na tuntuɓar Seddik ya ci-tura, sai daga baya ya tura masa wata gajeriyar amsa ta wayar salula yana cewa ai bakin alƙalami ya bushe. Rabbi Michel Serfati na mai ra´ayin cewa Jalloul Seddik ya gaza yin haƙuri.

Verletzte in Gaza nach israelischen Angriffen
Hoto: AP

“Saboda hotuna na ban tausayi kuma marasa kyaun gani daga Gaza haɗe da rahotanni da sharhuna da kafofin yaɗa labarai musamman na ƙasashen Larabawa suka riƙa watsawa game da rikicin na Gaza ya sa Jalloul Seddik ya canza shawara. Matsayinsa game da tattaunawa ko yin sulhu ya canza bayan fara yaƙin na Gaza. Ina ganin wannan abin baƙin ciki ne matuƙa da bai tuntuɓe ni ba don mu shawarta akan wannan batu.”

Kawo yanzu Jalloul Seddik ya ƙi yin hira da manema labarai game da murabus ɗin da yayi daga shugabancin ƙungiyar ta haɗin guiwa tsakanin Yahudawa da Musulman Faransa. Ya ce ba ya son ya ƙara rura wutar rikicin musamman a dangane da halin da ake ciki. Hatta shi kanshi kakakin babban masallacin birnin Paris ya ƙi cewa uffan kan murabus ɗin inda ya ce bau shafe su ba. A ƙarshe ya zargi ´yan jaridar ƙasashen yamma da cewa ba abin da suke yi illa shafawa Musulmai kashin kaza.

Rikicin na Gaza dai na ƙara janyo rashin jituwa, saɓani da kuma ƙiyayya tsakanin Yahudawa da Musulaman Faransa. Tun a ƙarshen watan Disamban bara ƙungiyoyin Yahudawa a Faransa ke ƙorafi game da ƙaruwar ayyukan ƙin Yahudawa da kuma hare-hare akan wuraren ibadarsu a cikin ƙasar ta Faransa. Suka ce hakan ya zama ruwan dare a ƙasar. To sai dai su ma Musulman sun kasance abin ƙyama a rayuwar yau da kullum ta ƙasar. Alal misali wasu da ake zargi ´ya´yan wata ƙungiyar tsagerun Yahudawa ne sun kai hari kan wasu yaran makaranta musulami su biyu a gaban makarantarsu dake birnin Paris, saboda sun ƙi karɓar wata ƙasida ta nuna goyon baya ga Isra´ila.

Hakazalika wani limami daga unguwar Drancy dake wajen birnin Paris wanda yayi suna bisa gudunmawar da yake bayar don samun fahimtar juna tsakanin Yahudawa da Musulmai ya sha da ƙyar lokacin da wasu suka farmasa a cikin motarsa, inda suka lalata motar. Ya sha samun wasiƙu na barazana ga lafiyarsa. Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ta Yahudawa da Musulmai ya ce ba wanda ya yi tsammanin cewa wani yaƙi a yankin Gabas Ta Tsakiya zai yi mummunan tasiri a tsarin zamantakewa tsakanin Yahudawa da Musulmai a Faransa. Ya yi nuni da cewa a cikin shekaru biyar da kafuwarta ƙungiyar su ta ba da gagarumar gudunmawa musamman ta shirya taruka kai da kai tsakanin Yahudawa da Musulmai tare da yin shawarwari tsakani don kawad da wariya da rashin jituwa. Ya ce kamata yayi wannan tuntuɓar juna ta ba da damar ci-gaba da tattaunawa a cikin irin wannan lokaci na rikice-rikice.

“Sau huɗu muna kai ziyarce-ziyarce ta haɗin guiwa wanda ya ba mu damar ziyartar wurare daban-daban har 150 a cikin birnin Paris da wajensa. A duk inda muka je mun shirya taruka na ƙarawa juna sani, wasannin kaɗe-kaɗe da cin abinci tare dukka da nufin kyautata fahimta da dangantaka tsakanin Yahudawa da Musulmai. Muna kai ziyara a masallatai da wuraren ibadar Yahudawa. A lokuta da dama Yahudawan da Musulman musamman matasa su kan nuna mana cewa waɗannan ziyarce ziyarce sun ba su damar sanin juna da ƙara fahimtar abubuwan da addinan biyu suka ƙunsa.”

Waffenruhe Israel Gaza Panzer im südlichen Israel
Hoto: AP

Rikicin tsakanin Isra´ila da Falasɗinawa ya kasance wani abin da ke sosawa masu matsanancin ra´ayi na sassan biyu wurin da ke yi musu ƙaiƙayi. Suna amfani da halin da ake ciki suna inganza magoya bayansu don su ƙi juna, inji shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ta Yahudawa da Musulman Faransan Rabbi Michel Serfati. Ya ce muhimmin abu shi ne ƙungiyar ta ci-gaba da aikinta duk da wannan mawuyacin hali da aka shiga.

“Bayan muraɓus ɗin na Jelloul Seddik, shugabannin ƙungiyoyin dake ƙarƙashinmu sun yi ta bugo mun waya suna masu tabbatar mun da cewa al´ummomin Yahudawa da Musulman za su ci-gaba da tafiyar da kyakkyawan aikin da suka fara har sai an cimma manufar da aka sa a gaba.”

Tsamin dangantakar tsakanin Yahudawa da Musulmai a Faransa ba zai sa shi ma Rabbi Serfati yayi watsi da ƙoƙarin da ake na samun fahimtar juna ba. Yana cikin shugabannin dake roƙo da kira da a samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya kana kuma yana kira da a yi amfani da motar ƙungiyar wajen bi unguwa-unguwa a Paris a wata yakuwa da nufin kyautata zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Musulmai.