Rikicin gas tsakanin Rasha da Ukraine. | Siyasa | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin gas tsakanin Rasha da Ukraine.

Rikicin samar wa kasar Ukraine makamashin hayakin gas da ya barke tsakaninta da Rasha, na bazanar yaduwa zuwa yankunan yammacin Turai. Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turan dai ta ba da sanarwar kiran wani taro na hukumomin kula da makamashi na kasashe 25 mambobinta, a ran 4 ga wannan watan wanda za a yi a birnin Brussels.

Ma'iakatar adana hayakin gas ta Ukraine.

Ma'iakatar adana hayakin gas ta Ukraine.

Kasar Amirka na cikin farkon kasashen ketare, da suka nuna nadamarsu ga matakin da kamfanin makamashin nan Gazprom na Rasha ya dauka, inda ya rufe bututun hayakin gas da ke samar wa kasar Ukraine wannan makamashin da take bukata kamar ruwa a jallo. Irin wannan matakin ba zato ba tsammani dai, zai iya janyo wani rudami a fannin samad da makamashi, abin da kuma zai iya zamowa wata damuwa ga huskar tsaro a yankin, inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amirkan Sean McCormick. A nasa ganin dai, Rasha na amfani da wannan rikicin da ya barke kan farashin hayakin gas din ne wajen angaza wa Ukraine din a siyasance.

Ita dai Rasha ta bayyana cewa, kamata ya yi Ukraine ta dinga biyanta farashin da ake biya a ko’ina a kasuwannin duniya na hayakin na gas, abin da kuwa ya ninka farashin da da take sayar wa Ukraine hayakin gas din sau biyar. Sai dai, wannan sabuwar shawarar da Rashan ta yanke, ta shafi kasar ta Ukraine ne kawai. Sauran kasashen tsohuwar tarayyar Sowiet, kamarsu Belaruss, na samun wannan makamashin daga Rashan ne a farashi na abokantaka, wato mai rahusa. Ban da dai Amirkan, darakta-janar na kungiyar Ciniki Ta Duniya, wato WTO, Francois Lamy, shi ma ya sanya alamar tambaya a kan wannan salon na Rasha.

A Kungiyar Hadin Kan Turai ma, ana gama gira game da wannan batun. Sai dai jami’an kungiyar na nuna halin diplomasiyya ne wajen bayyana damuwarsu. Kamar yadda wata kwamishina a sashen harkokin ketare na kungiyar, Benita Ferrero-Waldner ta bayyanar, kamata ya yi biranen Moscow da Kiew su yi kokarin samo bakin zaren warware wannan matsalar:-

„Yana da muhimmanci dai, a ce Rasha ta yi la’akari da halin da Ukraine ke ciki. Amma kuma, wajibi ne a ci gaba da tattaunawar. Duk kasashen biyu, masu samad da man fetur ne da gas – abin da ke da muhimmanci wajen tabbatar mana da hanyoyin samad da makamashinmu.“

A halin yanzu dai, Kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai na samo kashi 25 cikin dari na yawan hayakin gas da suke bukata ne daga kamfanin Gazprom na Rasha. Bututun da ke kai wannan hayakin zuwa yammacin Turai kuma, yana bi ne cikin kusan duk fadin kasar Ukraine din. Amma kwamishina Ferrero-Waldner ta ce kungiyar EUn ba ta huskantar wata barazana ga hanyoyin samo makamashinta na hayakin gas, duk da wannan rikin da ya barke. Sai dai, idan rikicin ya ci gaba da tabarbarewa, ba a samo hanyoyin warware shi da wuri ba, to za a iya jin barbashin sakamakon da zai haifar ma a nan Turai:-

„Duk wani matakin da zai janyo cikas, zai dusashe imanin da nahiyar Turai ke da shi ga masu ba da gas din. Za a sami rashin yarda da juna, idan aka gaza kiyaye ka’idodjin yarjejeniyoyin da aka cim ma.“

Ana dai kyautata zato a nan Turai cewa, lamarin ba zai kai ga hakan ba. Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turan, ta ba da sanarwar cewa, nan ba da dadewa ba, za ta kira wani taron masu kula da fannin makamashi na kasashe 25 mambobinta a birnin Brussels. Kwamishina Ferrero-Waldner ta bayyana cewa, a ran 4 ga wannan watan ne za a yi taron, kuma babu shakka, za a tattauna wannan batun.

A halin da ake ciki yanzu dai, kasashen kungiyar EU na da rarar hayakin gas din da suka tara da kuma masu samar mata wannan makamashin daga wasu yankuna daban. Amma duk da haka, kwamishina Ferrero-Waldner ta nanata muhimmancin da akwai, na sulhunta wannan rikicin ba tare da wani bata lokaci ba.