RIKICIN GARIN FALLUJAH | Siyasa | DW | 10.11.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RIKICIN GARIN FALLUJAH

FALLUJAH A YAU LARABA.

FALLUJAH A YAU LARABA.

Dakarun Amurka a Iraki sun wayi gari ayau Laraba da lasan takobin cewa nan da saoi 48 zasu ci galaba wajen kwace ilahirin garin Falluja daga hannun yan yakin sari ka noke,adai dai lokacin da wasu yan takifen da suka sace uku daga cikin yan uwan prime ministan Iyad Alawi,sukayi barazanar kashesu idan har baa daina afkawa falluja da wadannan kazaman hare hare ba.

Sai dai ayayinda ake cigaba da dauki ba dadi a wannan yankin,ana kuma cigaba da fuskantar tashe tashen hankula a wasu sassa daban daban na kasar ta Iraki,inda ko a yau din ma jamian tsaron kasar 6 da Sojan Amurka guda sun rasa rayukansu sakamakon fashewan bomb da aka dasa a gefen hanya,ayayinda wasu mutane dauke da makamai suka kutsa birnin Mosul daga arewaci.

Prime minista Alawi dai yayi alkawarin kawo karshen wadannan tashe tashen hankula kafin a gudanar da zaben kasa baki daya a watan janairu idan Allah madaukakin sarki ya kaimu,inda yake ganin cewa samun nasaran Fallujan zai zamanto wata dama ce na cimma burin daya sanya gaba.Sai dai a halin yanzu rikicin na neman rincabewa ,bayan da a jiya talata wasu mutane 3 a mota suka sace Dan uwansa Ghazi Allawi da mai dakinsa da matar dansa,ata bakin majiyar jamiiyar Alawin.Kungiyar dai tayi barazanar kashe mutane 3 dake hannunta cikin tsukin saoi 48,idan har bai Alawi bai dakatar da rikicin na Fallujah tare Prisononi,a wata sanarwa data fito ta naurar sadarwa ta yanar gizo gizo.

Ofishin Prime minista Iyad Alawi ya tabbatar da sace dan uwan nasa mai shekaru 75 da haihuwa,da surukarsa,sai dai babu wani batu dangane da maidakinsa da akace an saceta ita ma.An dai sace wadannan mutane ne a gidan Dan Uwan Prime ministan dake Kudancin Bagadaza.Kakakin fadar Gwamnatin Irakin ya bayyana cewa ire iren wadannan sace sacen mutane da akeyi domin garkuwa dasu,bazai dakatar da da yaki da akeyi da ayyukan tarzoma ba.

Wannan sabon rikici dai ya taso ne bayan da Dakarun Amurkan suka sanar da kutsawa tare da mallake Fallujan dake yammacin Bagadaza cikin tsukin kwanaki biyu.

Tun dai a ranar Litinnin ne dakarun kasar ta Iraki tare da na Amurka ,bayan umurnin Prime Ministan Iraki ke jibge a kewayen garin na Falluja.Ayau din dai wani jamiin Sojin na Amurka ya sanar dacewa ,yanzu haka kashi 70 daga cikin dari na kasar na karkashinsu,bayan kutsawa da sukayi daga arewaci,kuma sun dashi kudancin kasar.Ayayida yan yakin sari ka noken ke shirye domin mayar da martani wa kowane irin hari zaa afka musu da ita.yawancinsu na fake ne a gidaje da wasu gine gine,ayayinda wasu kuma ke masallatai,inda suke mayarwa dakarun Amurka dake harbinsu martani.

Rahotanni sun tabbatar dacewa Dakarun Amurka 11 dana Iraki 2 suka bakunci lahira a wannan dauki ba dadin na Falluja,ayayinda suma yan sari ka noken ,sun rasa rayukansu da dama.
Sai dai a yankunan gabashi da arewaci da yammacin birnin Mosul,an dauki tsauraran matakai na tsaro ,bayan harin da aka afkawa Ayarin Dakarun Amurka dake sintiri.

Yan darikar sunni da Shian Irakin dai sunyi tofin Allah tsine wa wannan tashin hankali da garin na Falluja ke fuskanta,wanda ya jagoranci ficewar jammiyar Sunni daga gwamnatin rikon kwaryan Irakin,wanda kuma ake gani wata barazana ce wa zaben kasar da ake shirin yi a watan Janairu.

 • Kwanan wata 10.11.2004
 • Mawallafi Zainab A Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvel
 • Kwanan wata 10.11.2004
 • Mawallafi Zainab A Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvel