1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Gabas ta tsakiya

August 8, 2006

Jakadu a Majalisar dinkin duniya na cigaba da kokari domin dakatar da yakin dake gudana a kasar Lebanon

https://p.dw.com/p/Btyk
Israila na cigaba da luguden wuta a Lebanon
Israila na cigaba da luguden wuta a LebanonHoto: picture-alliance/ dpa

A halin dai da ake ciki mayaƙan Hizbullah da dakarun sojin Israila na cigaba da gwabza fada a kudancin Lebanon yayin da a waje guda jakadu a majalisar ɗinkin duniya ke cigaba da ƙoƙari domin kawo ƙarshen taása da zubar da jini wanda ya ɗauki tsawon makwanni hudu ana yi. Ministocin ƙasashen larabawa na shirin yin jawabi ga kwamitin sulhu na Majalisar ɗinkin duniya a game da buƙatar da ƙasar Lebanon ta gabatar na yin gyara a daftarin ƙudirin domin kira a dakatar da faɗan cikin gaggawa, a daya bangaren kuma, Israila ta yi gargaɗin cewa zata faɗaɗa farmakin soji idan har matakan diplomasiyar suka gaza tsaida rokokin Hizbullah. Mayaƙan saman Israila sun raba ƙasidu dake gargaɗin jamaá dake datse a kudancin Lebanon, cewa zasu kai hari a kan dukkan wata mota dake zurga zurga a kudancin kogin Litani wanda ya haɗa da yankin kogin Tyre. Bayanan dake ƙunshe a cikin ƙasidun na cewa dukkan motar da aka gani, zaá ɗauke ta tamkar tana safarar rokoki ne da makamai ga yan taádda.

Maáikatan agaji sun baiyana cewa ana tsananin buƙatar abinci da magunguna a wannan yanki. Wata majiya daga sojin Israilan ta ce sojin ta uku sun rasa rayukan su wasu biyar kuma sun jikata a ƙauyen Dabel dake kudancin Lebanon. Ya zuwa yau sojojin Israila 62 ne aka kashe a ɗauki ba daɗin tun bayan da aka yi garkuwa da yan uwan su biyu wanda yan Hizbullah suka yi a ranar 12 ga watan Yulin da ya gabata, lamarin da ya kasance ummul habaisin wannan ɗauki ba daɗin dake wakana a ƙasar ta Lebanon.

Ministan tsaron Israila Amir Peretz yace ya yi umarnin yin taánadin farmakin ƙasa idan gamaiyar ƙasa da ƙasa suka kasa tursasawa Hizbullah ta daina harba rokoki zuwa cikin Israila wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula masu yawa da kuma jikata wasu da dama.

Matakan diplomasiya na kawo ƙarshen dabarwar ta ci tura bayan da ƙasar Lebanon ta soki lamirin daftarin Majalisar ɗinkin duniyar da gazawa wajen Umartar sojin Israila su janye baki ɗaya daga wuraren da suka mamaye a Lebanon.

ƙasar Faransa wadda tana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsara daftarin ta ce a shirye take ta amince da shawarar Lebanon wanda ya sami amincewar ƙasashe 22 na ƙungiyar ƙasashen larabawa wanda ya bukacin yin gyara ga daftarin ƙudirin. Ministan harkokin wajen Faransa Philippe Dousty Blazy yace tun da farko sai da suka shawarci Amurka cewa kada su gabatar da daftarin ƙudirin har sai sun ji baásin ƙungiyar ƙasashen larabawa.

Jakadan ƙasar Rasha a majalisar ɗinkin duniya Vitally Churkin yace ba zasu amince da daftarin da zai kasance mara maána ba ga ƙasar Lebanon domin zai ƙara haifar da yamutsi ne kawai. P/M Britaniya Tony Blair yace yana fatan zaá cimma yarjejeniyar yiwa daftarin kwaskwarima ya dace da bukatun bangarorin biyu.

Majalisar gudanarwar Lebanon wadda ta ƙunshi wakilai biyu daga Hizbullah ta amince da shawarar tura sojojin Lebanon 15,000 zuwa kan iyakar ƙasar idan Israila ta janye sojojin ta. P/M Israila Ehud Olmert ya baiyana shawarar da cewa mataki ne mai ƙarfafa gwiwa to amma sai an yi nazari a kan ta.

Barin wuta da aka yi a ranar Talatar nan wanda ke zama mafi muni tun bayan ɓarkewar rikicin, ya hallaka a ƙalla mutane 69 a kudancin Lebanon. Maáikatan agaji na cigaba da ƙoƙarin gano mutane 26 waɗanda suka ɓace bayan luguden wuta da ya ragargaza wasu manyan gine gine guda biyu a kudancin Beirut. Ministan harkokin wajen Israila Tzipi Livni ya yi kira ga P/M Lebanon Fuad Siniora ya share hawayen sa, ya yi ƙoƙari domin kawo ƙarshen rikicin gabas ta tsakiya. A birnin New York sakataren majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan ya sake nanata kira ga Israila da Hizbullah su martaba dokokin ƙasa da ƙasa don kare haƙƙin alúma.