1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Gabas Ta Tsakiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa

October 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvNY

Wani kusa na Baradan kungiyar Al-Aqsa ya rasu a wani farmaki ta sama da sojojin Isra´ila suka kai a wasu wurare da ake zargi na ´yan takifen Falasdinawa ne dake Zirin Gaza. Jami´an kiwon lafiya sun ce a duk tsawon daren jiya jiragen saman yakin Isra´ila sun yi ta yiwa Zirin na Gaza lugudan wuta. Wannan farmakin na sojin Isra´ila na matsayin ramuwar gayya ga hare haren makaman masu linzami da Falasdinawa masu gwagwarmaya ke kaiwa akan yankin Isra´ila. Ministan harkokin wajen Bani Yahudu Silvan Shalom ya ce za´a ci-gaba da daukar fansa bayan harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Hadera ranar laraba da ta wuce wanda yayi sanadiyar mutuwar Isra´ilawa 5. Harin dai shine na farko tun bayan janyewar Isra´ila daga Zirin Gaza a cikin watan satumba.