Rikicin Falasdinawa da Yahudawa | Amsoshin takardunku | DW | 22.08.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Rikicin Falasdinawa da Yahudawa

Tarihin Rikicin Falasdinawa da Yahudawa

Gidajen Yahudawa a Zirin- Gaza.

Gidajen Yahudawa a Zirin- Gaza.

Masu sauraron mu assalamu alaikum ,barkammu da sake saduwa a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da ke amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: Fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hannun mai sauraron mu a yau da kullum , Muhammadu Salisu Lukman da ke Federal Polytechnic Nassarawa ,P. M. B. 001 Jihar Nassarawa a Tarayyar Najeriya. Ya ce don Allah menene ummul’aba’isin rikicin gabas ta tsakiya ne? Wato tsakanin Falasdanawa da Yahudawa.

Amsa: Matsalar abin da ya shafi Yahudawa da dangantakarsu da gabas ta tsakiya dai wata aba ce mai dadadden tarihin gaske, dominkuwa tunkafin haihuwar Annabi Musa Alaihissalam, wato tun zamanin Annabi Ibrahim Alaihissalam , shi wanda yai rayuwa a wannan yanki da yanzu ake kira Falasdinu da Iraki da Siriya da Misra. To Annabi Ibrahim Alaihissalam yana da “Yaya guda biyu sune Annabi Ishaq da Annabi Ismail.Su Yahudawa suna danganta kansu a matsayin “yayan Annabi Ishaq. Sukuma Falasdinawa suna danganta kansu a matsayin yayan Annabi Ismail. Wannan ya nuna kenan Yahudawa ma suna da tushe a wannan wuri kamar yadda Larabawa ma suke da shi. Sabodahaka gabaki dayan su sun rayu a wannan wuri , rayuwa mai yawan gaske kafin mulkin mallaka daban-daban da suka ringa faruwa , wadanda suka zama sanadiyyar fatattakar wannan nan, wannan can, a kai ta dai fuskantar matsaloli.Saida takai a Duniya Yahudawa basu da matsuguni amma saboda tarihi yai halinsa , suka shiga kasashe daban-daban na Duniya suka zauna a ciki.

Alokacin yakin Duniya na daya ,kasar Israila ta shiga ayari ita da Birtaniya da Faransa da kuma kawayen su wadanda suka yaki daular Usmaniyya wadda take da hedikwata a Turkiyya, wadda kuma take da karfin fada aji a kasashen Musulmi. Sakamakon haka sai wannan yanki gaba ki daya ya zamanto karkashin mulkin mallakar Birtaniya da Faransa da kawayen su. Yahudawa kuma a duk inda suke saboda su tsiraru ne sai suka shiga kulle-kulle na yanda zasu kwaci kansu , su kuma mallaki kasar turawa ta koma hannun su. Wannan ya sa suka fito da tsari guda biyu.Na farko dai shine tsarin shiga cikin siyasar kasashen Turawa. Na biyu tsarin kutsawa cikin tattalin arzikin su. Wadannan dalilai ya sa akan dole Turawan suka tafi da su.

Daya daga cikin alkawarin da akai musu saboda gudun mowar da suka bayar har aka ci nasara , shine za a sama musu guri da za su kafa daular su . Dafarko an yi musu alkawari za a basu guri a Uganda tunda dai Birtaniya ce take mulkin mallaka a wannan kasa,sai suka ce a a, sai dai inda su a addinance, addinin su ya basu ce war nasu ne, gurin su na alkawari,wato wannan yanki na Israila yanzu. To haka kuwa aka tsaga wannan guri , musamman bayan yakin Duniya na biyu, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta zauna da gindin ta.

Kasancewar kasashen da ke cikin majalisar a wancan lokaci ba ‘yantattu ba ne, a ka je aka yi rufa-rufa, aka tsaga yankin falasdinu ,aka ce to wannan shine yankin da ya shafi Yahudawa ,kuma su je su zauna a gurin. A wannan lokaci Majalisar Dinkin Duniya ta ce idan Yahudawa da Falasdinawa sun karbi wannan tsagu da aka yi, inda aka baiwa Yahudawa kashi hamsin da biyar daga cikin dari na Falasdinu, su kuma Falasdinawan a ka ba su kashi arbain da biyar cikin dari. Sannan kuma aka ce garin Kudus saboda mahimmancin sa a dukkanin addinan Musulunci da Kiristanci da kuma Yahudanci,zai kasance karkashin kulawar kasashen Duniya , bawai ya na karkashin Falasdinu ko Israila ba.

A wannan lokaci Israila wadda ita ruwa ne ya ciyo ta , kome aka mika mata zata karba, ballantana a ce an ba ta wannan gagarumar ganima,sai ta ce ta amince. Saboda haka sai akai mata rigista , ta zamanto daya daga cikin kasashe mambobi a cikin Majalisar Dinkin Duniya.Su kuwa Falasdinawa suka ce ba su yarda ba , wannan ai cuta ce,akan me za’a tsaga wurin su a baiwa yahudawa? Kuma harma sauran kasashen larabawa su ka goya musu baya , suka kuma sha alwashin kwato musu ‘yancin su , ko da tsiya ko da arziki.To daga wannan lokaci ne artabu ta fara faruwa , aka ci gaba da rikici da rigingimu har ya zuwa yau.

A wancan lokaci da Falasdinawa sun yarda sun karbi wannan kashi arba’in da biyar a bisa zaluncin da aka yi musu, to da yanzu akwai wani abu mai suna daular Falasdinawa ‘yantacciya. Rashin karbar da suka yi, shi ya sa Isra’ila ta ci gaba da yakarsu da kuma mamayar sauran yankin na Falasdinawa, wanda a cikin wannan kashi arba’in da biyar din , a binda Falasdinawa suke hakilon su samu yanzu bai wuce kashi ashirin ba. kuma Isra’ilan tana ki , ballantana kuma abinda ya shafi kudus din da ta ce ya zama nata wanda hakan ya sa akullum ake ci gaba da wannan gwagwarmaya ta siyasa, Isra’ilan na samun goyon bayan Amurka ,su kuma Falasdinawa ba su da wan ceto,domin kuwa su kansu Larabawan sun juya musu baya, hasalima dai ta kansu suke yi domin su samu karbuwa awajen Amurkan kada su bata mata rai, wanda kuma indai da haka ne to ba’a san ranar da za’a iya kawo karshen wannan matsala ba.

 • Kwanan wata 22.08.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BwXS
 • Kwanan wata 22.08.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BwXS