Rikicin dokar kwadago a Faransa | Labarai | DW | 31.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin dokar kwadago a Faransa

A yau ne shugaban kasar faransa Jacques Chirac zai yiwa alúmar kasar jawabi a game da sabuwar dokar kwadago da ta haddasa gagarumin yajin aiki na gama gari a kasar Faransa. Babbar kotun kasar ta baiyana dokar da cewa halastacciya ce. Tuni majalisar dokokin kasar ta zartar kudiri na amincewa da dokar. A yanzu dai shugaban kasar Jacques Chirac na wani hali na tsaka mai wuya, walau dai ya sanya hannu a kan dokar ko kuma yaki amincewa da ita. P/M Faransan Dominique de Villepin wanda a yanzu farin jinin sa ya fara dusashewa a sakamakon dokar, yace wajibi ne a aiwatar da ita domin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa. Dokar dai ta saukaka daukar matasa aiki da kuma sallamar su cikin sauki ba tare da bayani ba a farkon shekaru biyu na sanin makamar aiki. Miliyoyin maáikata da kungiyoyin dalibai sun gudanar da zanga zanga a birnin Paris da sassan kasar Faransa domin nuna adawar su tare da bukatar gwamnati ta janye dokar wadda suka baiyana da cewa doka ce ta kama karya.