1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin datsewar Gaza

Isra'ila ta fara duba bukatun kasashen duniya, na ta bude mashigar zirin Gaza.

default

Palasdinawa dake jiran agaji

Majalisar Ministocin Isra'ila  ta yi zaman taro don sassauta takunkumin da ta ɗora wa zirin Gaza tun shekarar 2006.

Taron wanda aka gudanar a bayan fage batare da an cimma  tudun da fawaba, duk da rahotanin da aka riƙa samu da farko cewar ministocin za su ƙada ƙuri'a akan shawara haɗin gwiwa da aka bayar maƙonni da dama da suka wuce, na gana wa tsakanin firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da wakilin kafofi hudu na sasanta rikicin yanƙin gabas ta tsakiya Tony Blair na Birtaniya.

Wani Jami'in Gwamnati ya bayyana cewar an kai tsawon sa'o'i takwas ana tattaunawa tsakanin ministoci 15 tare da tsaida shawarar sake haɗuwa yau Alhamis, don ci gaba da tattaunawan. ko da yake jami'an sun ki bayyana abunda tattaunawar tasu ta ƙunsa, amma duk da haka ana saran cewar  za'a tattauna batun rikicin da ya shafi zirin na  Gaza . Bisa daidaituwar da aka cimma tsakanin Tony Blair da firaim minista Netanyahu. Isra'ila zata yi sassauci dan gane da wasu kaya da ba a shigarwa zirin Gaza, tun bayan da Isra'ila ta aza mata takunkumi a shekara ta dubu biyu da shida .

Baya ga kayan bukatun yau da kullum, in har majalisar ministocin ta Isra'ila  ta albarkaci wannan daidaituwa za a kuma shigar da kayan gini domin tafiyar da wasu shirye shirye da majalisar ɗinkin duniya ta tanadar.

Isra'ila dai ta sha fuskantar kira data janye wannan takunkumi, musamman bayan farmakin da sojojinta suka kai kan jiragen ruwan taimako ga zirin Gaza, in da suka halaka wasu jami'an taimakon guda tara yan asalin ƙasar Turkiya, kuma dai dai lokacin da gwamnatin Isra'ila ke na zari game da sassauta takunkumin, a ɗaya ɓangaren kuma ana ta samun masu yin kira game da gudanar da bincike a kan matakin na sojan Isra'la.

Bisa ta bakin Norman Peach, tsofon wakilin jam'iyyar gurguzu a majalisar dokokin Jamus kuma kwararren masani akan tsarin dokoki na kasa da kasa, wanda kuma ya kasance a cikin daya daga jiragen ruwan da sojan Isra'ila suka kai musu hari a karshen watan mayun da ta wuce, yace wajibi ne wata hukuma ta kasa da kasa ta gudanar da bincike akan wannan tabargaza.

Ya ce: “Wajibi ne wannan hukuma ta kunshi kwararrun masana daga kasashe daban-daban, wadanda zasu gudanar da bincike akan abin da ya faru ba tare da shisshigin wata gwamnati ba. Domin tabbatar da gaskiyar sakamakon binciken kamata ya yi hukumar ta tuntubi sojojin Isra'ila dake da hannu a mataki da kuma fasinjojin jirgin da tsautsayin ya rutsa dasu, musamman ma wadanda suka ji rauni daga cikin da kuma wadanda Isra'ila ta tsare. Dukkan wadannan ya kamata a ji ta bakinsu.“

Mawallafiya: Husseina Jibrin Yakubu

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal