Rikicin Darfur | Labarai | DW | 22.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Darfur

Rikicin yankin Darfur na daya daga batutuwan da a ke kai ruwa rana kansu a halin yanzu a dandalin diplomatia na dunia.

Idan ba a manta ba, ranar laraba da ta wuce, komitin wanzar da zaman lahia, na ƙungiyar taraya Afrika, ya gudanar da zaman taro a birnin New York, inda ya bayyana tsawaita wa´adin dakarun AU, a yankin Darfur har zuwa ƙarshen wannan shekara.

A nasa gefe shugaban kasar Amurika Georges Bush ya nada Andrew Natsios a matsayin wakilin mussamman a Darfur.

Cemma jami´in, massani ne na harakokin yankin, ta la´akari da shekaru da dama, da ya share, a matasayin shugaban hukumar bada agaji ta Amurika wato, USAID a ƙasar Sudan.

Wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia a Darfur Jan Poronk,shima, ya bayyana wajibcin farfaɗo da yarjejeniyar zaman lahia da ta rattaba wa hannu:

„Yarjeniyar zaman lahiar Darfur na cikin yanayin rai kwakwai, mutu kwakwai.

Duk abinda ke cikin halin suma, ya kusa mutuwa.

Hakan ta wakana domin ba a dauki inganttatun matakai na kula da yarjejniyar ba“.