Rikicin Darfur | Labarai | DW | 30.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Darfur

Amnystie International, ta yi kira ga ƙungiyar haɗin kann ƙasashen larabawa, ta yi ruwa da tsaki, a game da batun samar da zaman lahia a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

A ganawar da shugabar Amnystie Irene khan ta yi da Sakarate Janar na ƙungiyar ƙasashen larabawa,Amr Musa, ta bayyana mahimamcin wannan ƙasashe, wajen kawo ƙarshen rikicin Darfur.

A yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana, a game da rikicin Darfur, hukumomin Kahartum, sun jaddada aniyar su, ta cika alkawarin da su ka ɗauka, tare da yan tawayen gabacin wannan ƙasa.

A game da haka ne, gwamnatin ta bayyana naɗa 3 daga shugabanin tawaye, a manya-manyan muƙamai.

Wanda aka naɗan, sun haɗa da, Musa Mohamed Ahmed, Mabruk Mubarak Salim, da kuma Amna Dirar, da aka ba matsayin ƙaramar minista, mai kulla da suhuri.

ƙungiyoyin tawayen gabacin Sudan, sun ƙudurci ajje makamai, ranar 1 ga wata mai kamawa.