Rikicin Darfur | Labarai | DW | 25.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Darfur

Darfur

Gwamnatin sudan ta dakatar da ayyukan hukumar mdd a lardin Darfur,bayan zargin datayiwa majalisar da daukan nauyin sufurin shugaban kungiyar adawar,dataki amincewa da yarjejeniyar sulhu da aka cimma.Mdd ce dai ke gudanar da mafi yawan ayyukan agaji a Darfur,tare da kulawa da harkokin lafiya da kare hakkin biladama da samar da Abinci,a ilahirin wannan yanki da fadinsa yakai girman kasar faransa.Kakakin maaikatar harkokin waje na Sudan Jamal Ibrahim ,ya sanar dacewa ,wannan mataki da gwamnati ta dauka ya shafi dukkan yankunan Sudan,kuma zaa cigaba da wannan mataki ,har sai sun samu bayanai masu gamsarwa.Ya fadawa manema labaru cewa an dauki wannan mataki ne,saboda wani jirgin saukan ungulu na mdd ya dauki shugaban adawa Suleiman Adam Jamous ,wanda yaki rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu da aka cimma a ranar 5 ga watan Mayu,ba tare da majalisar ta tuntubi gwamnati a Khartum ba.To sai dai kakakin gwamnatin yace,wannan takunkumi bai shafi hukumar bada tallafin abinci ba,da kuma mai kula da kananan yara ta UNICEF.To sai kawo yanzu kakakin mdd,ta sanar dacewa har yanzu baa gabatar musu da wannan takunkumi ba,a hukumance.