Rikicin Darfur | Siyasa | DW | 14.03.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Darfur

Rikicin yankin Darfur na shirin ɗaukar saban sallo

default

Ƙasashe da ƙungiyoyin daban-daban na dunia, na ci gabada matsa ƙaimi ga shugaba Omar El Bashir na ƙasar Sudan a game da halin ƙuncin rayuwa da al´ummomin yankin Darfur su ka tsinci kan su a ciki.

Idan da za a iya tunawa ranar litinin da ta gabata, hukumar MDD mai kulla da kare haƙƙoƙin jama´a ta gabatar da wani rahotaniu mai bantausayi, inda ta bayyana dalla-dalla, ukubar da hukumomin Khartum ,ke ganawa al´ummomin Darfur.

Oiishin sakatariyar harakokin wajen Amurika ya hiddo wani rahoto inda ya bayana cewar a yanzu fa kur ata kai bango Amurika da wasu ƙasashen dunia, sun gaji da wasa da hankullan su da shugaban El Bashi ke yi a game da wannanbatu.

Kakakin gwamnatin Amurika Tom Casey, ya ce haƙuri ma, ya na da iyaka, a game da haka, bayan wata da wattani a na kai ruwa rana, yanzu ,

lokaci yayi na ɗaukar matakan da su ka dace, domin cilastawa gwamnatin Sudan ta amince da karɓar rundunar shiga tsakani ta Majalisar Ɗinkin Dunia.

Itama gwamnatin Britania ta bayyana goyan baya ga matakin da Amurika ke bukatar ɗauka, wanda ya haɗa da shata iyakar shiga tsakani a yankin Darfur.

Jikadan Britania a Majalisar Ɗinkin Dunia, Emyr Jones Parry ya ce yanzu kam mataki ɗaya da ya rage shine na hukunci mai tsanai ga Sudan, a game da haka ya tabatar da cewa a cikin wannan mako,Britania zata gabatar wa komitin sulhu wani daftarin da zai bayana dalla-dalla matakan hukucin.

Jikadan ya maida martani ga wasikar shugaba El Beshir a komitin sulhu wadda ta jadada manufofin hukumomin Khartum na ƙin amincewa da rundunar shiga tsakani ta MDD.

A nata ɓangare, gwamnatin France ta yi kira ga shugaba El Beshir, yayi wa Allah da annabin sa, ya ceci rayukan al´ummomin Darfur, ta hanyar dakatar da kai hare-haren kan mai uwa da wabi, da kuma bada damar aika rundunar shiga tsakani.

Dakarun kungiyar tarayya Afrika da ahalinyanzu ke gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro ayankinna fuskanatr matsalolin ƙarancin kayan aiki, da sojoji, a game da haka Rwanda ɗaya daga ƙasashen da su ka tura dakaru a Darfur ta yi barazanar janyewa, muddun ba a ciwo kan wannan matsaloli ba.

 • Kwanan wata 14.03.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btw1
 • Kwanan wata 14.03.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btw1