1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Darfur na shirin ɗaukar saban sallo

March 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuPe

Ƙasashe da ƙungiyoyin daban daban na dunia na ci gaba da matsa ƙaimi ga shugaban ƙasar Sudan Omar El Bashir, a game da rahoton Majalisar Ɗinkin Dunia mai bayyana wulaƙancin da hukumomin Khartum ke yi wa al´umomin yankin Darfur.

Amurika da Britania sun hiddo sanarwar yiwuwar ɗaukar mattakai tsatsaura, a kann Sudan muddun ta ƙi amincewa da karɓar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.

Kazalika ƙasar France ta aika wasiƙa a ranar jiya, inda ta bayyana rashinamincewa da matakin fadar mulkin gwamnatin Sudan a game da wannan rikici.

Ya zuwa yanzu, Shugaba El Bashir ta bakin ministan shari´a Mohamed Ali Elmardi, yayi watsi da rahoton na Majalisar Dinkin Dunia, a game da tozarcin da ke wakana a Darfur.

A wani labarin kuma, ƙasar Rwanda ta yi barazanar janye dakarun ta daga wannan yanki, ta la´akari da karancin kayan aiki da rundunar shiga tsakani, ta tarayya Afrika ke fuskanta.

Gobe idan Alllah kai mu, komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, zai shirya zama na mussamman, a game da rikicin ƙasar Sudan.