1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Britania da Iran

April 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuOa

A na ci gabada kai ruwa rana tsakanin Britania da Iran a game da sojojin ruwan Engla 15 da Iran ta capke tun ranar 23 ga wata Maris da ya gabata.

Bayan taron ministocin harakokin wajen ƙungiyar gamayar turai wanda ya bada cikkaken goyan baya ga GwamnatinTony Blair, ministan harakokin wajen Iran Manoucher Motaki ya yi kira ga hukumomin London, su daina cussa siyasa a cikin wannan al´amari, wanda a cewar sa, batu ne, na karya dokokin ƙasa da ƙasa.

A halin da ake ciki, Iran ta bayana aniyar gudanar da bincike, da kuma gurfanar da wannan sojoji gaban ƙuliya tare da yanke masu hukuncin da ya dace, a game da zargin da ta yi masu, na shiga harabar ruwan ta, na tekun Golf ba tare da izini ba.

A karro na farko, shugaban ƙasar Amurika Georges Bush ya hurci a dangane da wannan cece-kuce, inda ya yi Allah wadai da kama sojojin , to amma ya buƙaci a warware al´ammarin ta hanyar diplomatia.

Duk da haɗin kan da Britania ke samu, a kan wannan rikici, ministar harakokin wajen Britania Margaret Beckett, ta bayyana fargabar, samun belin sojoji 15 cikin gaggawa