1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Bakassi ya zo ƙarshe

Yahouza, SadissouAugust 18, 2008

Nigeria ta miƙawa Kamarau tsibirin Bakassi, bayan shekaru 15 na taƙƙadama.

https://p.dw.com/p/F0Io
Sojojin Nigeria sun fita daga Tsibirin BakassiHoto: AP


A wannan karo, shirin zai duba batun yankin Bakassi, wanda Tarayya Nigeria ta miƙawa Kamaru ranar 14 ga watan Ogusta na shekara ta 2008, bayan shekara da shekaru ana kai ruwa rana.

Tsibirin Bakassi na da murrabba´in Kilomta dubu ɗaya, kuma ƙiddidiga ta gano cewar, al´umma kimanin dubu 30 zuwa 40 mafi yawansu masunta, kokuma masu kamun kifi, ke rayuwa a cikin wannan ruwa, da aka jimma  ana taƙƙadama akai tsakanin Nigeria da Kamaru.

Tun shekara ta 1913 turawan mulkin mallaka, wato Britaniya da Jamus, suka rattaba hannu akan yarjejeniyar da ta shata iyaka tsakanin Nigeria da Kamaru.

Kamar sauran yankunan Afrika,ƙasashen biyu sun fuskanci matsaloli a game da wannan iyaka.

A shekara ta 1993 rikicin yayi ƙamari bayan da sojojin Nigeria suka mamaye wanu garuruwa na yankin Bakassi mai arzikin man petur da Gaz.

A watan Maris na shekara ta 1994 ƙasar Kamaru, ta shigar da ƙara gaban kotun ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta zargi Nigeria ta mamaye mata wasu yankuna da ta mallaka.

Bayan shekaru takwas ana ta ci bata ciba , a ƙarshe dai kotun ta yanke hukunci a watan Oktober na shekara ta 2002.

Sakamakon hukunci ya hallata yankin Bakassi ga ƙasar Kamaru, a game da haka, Kotun ƙasa da ƙasa ta umurci Nigeria ta fita daga wannan ruwa.

To saidai duk da wannan hukunci, an cigaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin ƙasashen biyu masu maƙwabtaka da juna.

A wani yunƙuri na riga kafi ga ɓarkewar yaƙi, ƙasar Amurika ta shiga tsakani ta hanyar shirya wani taro na mussamman,  da ya haɗa shugabanin ƙasashen Nigeria da na Kamaru.

Ɓangarorin biyu, sun cimma masalahar da aka raɗawa suna yarjejeniyar Greentree, wani gari dake kussa da birnin New York na Amurika.

A sakamakon wannan yarjejeniyar Nigeria ta fara janye sojojinta daga yankunan da ta mamaye ranar 12 ga watan Juni na shekara ta 2004, ta kuma alƙawarta bi sau da ƙafa hukunci da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yanke, wanad ya umurce ta ta fita daga Bakassi, kamin 14 ga watan Ougusta na shekara ta 2008.

Hausawa kan ce kyan alkwari cikawa, shugabanTarayya Nigeria Alhaji Umaru Musa ´yar Aduwa ya cika alƙawarin da ƙasarsa ta ɗauka, albarkacin wani ɗan ƙwarƙwarya biki da aka shirya inda a hukunci Nigeria ta miƙawa Kamaru yankin Bakasi.

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya  na yankin yammacin Afrika, Said Jinit, ya bayyana matuƙar gamsuwa a game da wannan hali na dattako da hukumomin Nigeria suka nuna wanda kuma cewar sa, ya zama abun misali ga sauran yankunan Afrika dake fama da rigingimun iyakoki.

da dama daga jama´a na da ra´ay cewar wannan mataki zai kara daga tutar Nigeria a idanun duniya, to saidai a cewar Antohny Jannar na Nigeria,Michael Aondoakaa, ɗaga martana  kokuma akasin haka, cilas ne Nigeria ta bi dokokin ƙasa da ƙasa:Batu ne na shari´a da kotun ƙasa da ƙasa ta yanke, kuma wajibi ne ga Nigeria ta bi wannan umurni kasancewar ta ƙasar da ta rattaba hannu a kan dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Batun wannan mataki ya ɗaga tuta Nigeria, ko ya dakushe ta bai taso ba , maganar gaskiya itace kawai Nigeria ta bi dokokin ƙasa da ƙasa.

Aboya Manase Endong,Professa ne a jami´ar Kamaru, kuma ƙurrare ta fannin harakokin  siyasa da na diplomatia, ya bayyana dalilan da suka sa Nigeria da Kamaru ke taƙƙadama  akan tsibirin Bakassi:Tsibirin Bakassi na da matuƙar mahimmanci ga Kamaru, ta fannin tattalin arziki.

Bincike ya gano cewar ya na kunshe da ɗimbin arzikin Man petur, Gaz da kuma kifi.

A ɗaya wajen Professa Endong ya yabawa matakin sulhu da ƙasashen biyu suka cimma wajen warware wannan rikici ba tare da ɓarkewar yaki ba, kamar yadda aka saba gani a wasu ƙasashen duniya.

wannan mataki zai taimaka inji shi aka ra ƙarfafa cuɗaya tsakanin al´umomin Nigeria da Kamaru.

A gani na matakin da shugabanin suka ɗauka na yin amfani da dokoki da hanyoyin diplomatia, za su taimakawa wajen ƙarfafa mu´amila cikin fahintar juna, kuma ya zama wajibi, ga dukkan ƙasashen biyu su bi hanyoyin da suka dace, domin ƙarfafa zumunci, ta yadda zasu buɗa wani saban babe na danganta mai ƙarfi.

To tunnni dai Nigeria ta miƙawa Kamaru Bakassi, kuma a cewar mai Martaba Etinyin Etin Okon Edet, sarkin Bakassi, a halin da ake ciki, komai  na tafiya lau lami a yankin cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kamar yadda hukunta na Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ya bada tanada da dama daga mazauna Bakassi masu shawar komawa Nigeria sun ƙaura daga yankin da, zuwa wasu sabin yankuna mallaka Nigeria,a game da haka mai martaba Sarki yayi kira, domin samar da taimakon ga wannan jama´a: Muna buƙatar taimako gada gwamnatin Tarayya da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya, domin  har ya zuwa yanzu bamu gani ba a ƙass, ta fannin taimakon da Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙasashe masu hannu da shuni, suka alƙawarata tallafawa al´ummomin Bakassi.

Muna  buƙatar taimakon kuɗaɗe, domin samar da matsugunai ga mutanen da suka buƙaci komawa Nigeria, da kuma basu damar cigaba da kamun kifi kamar yadda suka saba.

 A ɓangaren ƙasar Kamaru, gwamntin shugaba Paul Biya, tayi tanadi matakai da dama, domin inganta rayuwar mazauna yankin Bakassi da suka zabi tsaya ƙarƙashin mulkin Yaounde.

Gwamnati ta ambata gina makarantu, asibitoci da kuma tallafi ta fannin sana´o´i da dai sairan ayyuka na inganta rayuwar yau da kullum.