1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Amirka da Rasha kan Siriya na zafafa

Yusuf Bala Nayaya
April 11, 2018

Amirka da Rasha na ci gaba da kallon juna cike da tuhuma, wace kasa ce ke da hannu a amfani da makami mai guba wajen kai hari a Siriya, lamarin da ke sake samun koma baya a zaman Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2vrrY
USA  Wassili Nebensja , UN-Sicherheitsrat zu Syrien
Wassili Nebensja jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Hoto: picture alliance / Julie Jacobson/AP/dpa

Kwamitin Sulhu na MDD ya yi watsi da bukatar da Rasha ta bijiro da ita kan masu bincike daga kungiyar da ke fafutikar haramci da amfani da makami mai guba dangane da zurfafa bincike kan wanda ke da hannu a amfani da makamin mai guba a Douma da ke wajen babban birnin Siriya a karshen mako. Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ya ce gwamnatin Shugaba Trump ce ke son kafar ungulu ga shirin bincike ta yadda za ta yi gaban kanta ta ce ga wanda ke da hannu wajen kai harin me guba a Siriya.

Amirka da Birtaniya da Faransa dai sun ki goyon bayan matakin na Rasha da suka ce matakin bai cika sharuda ba na sabbin hanyoyi da a ke bi wajen binciken amfani da makamai masu guba. Shugaba Trump dai ya ce za su kai wa 'yan ta'adda hari a Siriya.