Rikicin addini a Nigeria | Labarai | DW | 14.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin addini a Nigeria

Mutane aƙalla takwas sun rasa rayukansu a rikicin addini da ya ɓarke a jihar Tarabba ta tarayyar Nigeria.

default

Aƙalla mutane takwas sun rasa rayukansu a wani rikicin addini da ya ɓarke a Wukari da ke jihar Tarabba ta tarayyar Nigeria. Komishinan 'yan sandan jihar wato Aliyu Musa ya shaida ma kanfanin dillacin labaran Reuters cewa ƙura ta lafa a halin yanzu. Amma kuma sa'o'i da dama musulmi da kuma kiristocin garin na  Wukari suka shafe suna bai wa hamata iska, biyowa bayan ƙona wani masallaci da kristocin suka yi.

Su dai kiristocin suke ce sun ɗauki wannan mataki ne domin nuna rashin jin daɗinsu da gina masallaci a unguwar da ke da rinjayen kirista da a ka yi. Nigeria da ta ƙunshi mutane sama da miliyon 150 ta jima ta na fama da rarrabuwan kawunan tsakanin musulmi da krista a ƙasar. Ɗaruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a cikin wannan shekara a jerin rikice-rikicen ƙabilanci da na addini da Nigeria ta fiskanta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu