Rikicin ƙabilanci a Tchad | Labarai | DW | 09.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin ƙabilanci a Tchad

Wakiliyar hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla da yan gudun hijira a ƙasar Tchad, Helene Caux, ta ce fiye da mutane 200 su ka rasa rayuka, a sakamakon faɗan ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin larabawa, da saurann ƙabilu a gabancin ƙasar Tchad.

Al´umumomin wannanyanki na rayuwa cikinfaduwar gabatun ranar asabar da ta wuce.

Shima ministan sadarwar na kasar Tchad, ya bayyana abkuwar wannan rikici ba tare da ƙayyade yawan mutanen da su ka rasa rayuka ba.

Ministan ya tabatar da cewa, gwamnati na iya ƙoƙarin ta, domin kawo ƙarshen wannan tashe-tashen hankulla.