Rikicin ƙabilanci a Kirigistan | Labarai | DW | 13.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin ƙabilanci a Kirigistan

An kafa dokar hana fita a yankin da ake fama da rikici na ƙasar Kirgistan

default

'Yan ƙabilar Usbekistan a kusa da kan iyakar Kirgistan da Usbekistandake kudancin Kirgistan don nema mafaka a Usbekistan

Bayan mummunar tarzoma da aka fuskanta a kudancin ƙasar Kirgitsan, gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar ta kafa dokar hana fita na tsawon sa'o'i 24 a yankin da ake fama da rikicin. To sai dai duk haka rahotanni daga birnin Osh mai fama da rikicin ƙabilanci sun nunar da cewa wasu matasa sun cunnawa gine gine wuta a yau Lahadi. Waɗanda suka shaida abin da ya faru sun ce ana cikin wani yanayi mai kama da na yaƙi. Da farko rikici ya bazu zuwa yankin Jalalabad da wasu wurare na ƙasar. Mutane kimanin 100 aka kashe sannan fiye da 1000 sun samu raunuka sakamakon tashin hankalin da ya fara a ranar Alhamis da ta wuce. Shugabar riƙon ƙwarya Rosa Otunbayeva ta zargi magoya bayan hamɓararren shugaban ƙasa Kurmanbek Bakiyev da hannu a rikicin na ƙabilanci to amma ya yi watsi da wannan zargi. A kuma halin da ake ciki ƙasar Usbekistan ta ce 'yan gudun hijira dubu 32 daga Kirgistan sun shiga ƙasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmed Tijani Lawal