Rikicin ƙabilanci a Kirgistan sakamakon ɓarkewar tarzoma | Zamantakewa | DW | 14.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rikicin ƙabilanci a Kirgistan sakamakon ɓarkewar tarzoma

Dubban al'uimar Uzbek a Kirgistan sun yi gudun hijira zuwa makwabciyar ƙasar Uzbekistan

default

An ƙone gidaje a birnin Osh, na ƙasar Kirgistan bayan rikicin da ya ɓarke.

Dubban al'umar Uzbek na yin ƙaura suna ficewa daga yankunansu domin kauce ma faɗan da ya ɓarke a Kyrgyzstan wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane fiye da ɗari ɗaya, lamarin dake zama rikicin ƙabilanci mafi muni tun bayan ƙarshen tarayyar Soviet. 

Halin da ake ciki a kudancin Krygyztan ya ta'azzara inda musayar wuta da bindigogi da ta wakana tsakanin wasu ƙungiyoyi biyu dake hamayya da juna ta jefa biranen cikin wani wadi na fagen daga. Tsawon kwanaki uku matasa ɗauke da makamai suka yi ta bankawa ƙauyuka wuta da kashe kashen rayuka.

Ƙasar Uzbekistan wadda ke maƙwabtaka da Kyrgyzstan ta ce 'yan ƙabilar ta Uzbek su kimanin 100,000 ne yawancin su mata da ƙananan yara suka yi gudun hijra suka baro Krygyzstan inda a halin yanzu aka tsugunar da su a wani sansani na wuci gadi akan iyakar ƙasar. Ƙungiyoyin agaji sun yi kashedi game da taɓarɓarewar rayuwar al'uma. Andrea Berg ta ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta nan Jamus ta yi bayani tana mai cewa

" Tace na sami waya daga Uzbekistan musamman daga yankunan karkara waɗanda suka shaida min cewa ana ta harbinsu da bindiga. An yiwa mata fyaɗe, an kuma yiwa ƙananan yara kisan gilla, suka ce ba za su iya fita daga gidajensu ba, idan kuma suka yi yunƙurin fita akan bi su da harbi a baya. Babu dai sauƙi domin ta ko ina basu tsira ba".

' Yan ƙabilar Uzbek marasa rinjaye dake kudancin ƙasar sun sha nanata kira ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta samar da kariya a tsakanin iyakar da ta raba al'umomin biyu, amma gwamnatin ba ta nuna wata aniya ta ɗaukar wannan mataki ba.

Jami'ai sun ce mutane kimanin 113 suka rasu a tarzomar ta kwanaki uku yayin da wasu mutane 1,400 kuma suka sami raunuka. Tarzomar dai ita ce mafi muni tun bayan da aka hamɓarar da gwamnatin shugaba Kurmanbek Bakiyev a watan Aprilun da ya gabata.

A yanzu dai gwamnatin riƙon ƙwarya ta shugaba Roza Otunbayeva ta kafa dokar ta ɓaci a gundumar Osh inda daga nan ne tarzomar ta samo asali. An kuma faɗaɗa dokar ya zuwa wasu sassa a faɗin kudanci ƙasar musamman kudancin yankin jalalabad inda a nan ma tarzomar ta yaɗu.

Superteaser NO FLASH Kirgistan Kirgisien Unruhen

Tarzomar rikici a Kirgistan

Babban ƙalubale a cewar Andrea Berg ta ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Jamus ita ce yadda za'a taimakawa mutanen da a yanzu suka sami kan su cikin hali na ƙaƙa-nika yi.

" Haƙiƙa akwai batu na taimakon jin ƙan al'uma, yadda za'a kai ɗauki don taimakawa 'yan gudun hijirar cikin hanzari musamman da Tantuna da abinci da kuma magunguna. Akwai dai mutane da dama waɗanda suka jikata waɗanda aka samu aka kai su kan iyaka kuma suna buƙatar taimako na kula da lafiya".

Tsohon shugaban ƙasar ta Kyrygyzstan wanda yanzu haka yake gudun hijira a Belarus ya musanta zargin cewa yana da hannu a wannan rikici, yana mai cewa abin kunya ne kuma ƙarya ce tsagwaronta gwamnatin ke masa.

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya baiyana damuwa da girman wannan tarzoma da kuma yadda ta yaɗu. Shi ma shugaban ƙasar Rasha Dmitry Medvedev ya yi kira ga ƙasar ta Kyrgyzstan ta yi ƙoƙarin tabbatar da doka da oda ba tare da jinkiri ba.

Mawallafa : Christina Nagel / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Mohammed Nasir Awal