1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙidayar jama´a, a tarayya Nigeria

March 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv41

Jami´an tsaro a Tarayya Nigeria, sun bada sanarwar capke mutane 82, a faɗin ƙasar baki ɗaya, bayan an tuhume su da shirya ƙafar angullu ,ga al´ammuran ƙiddayar jama´a, da aka fara tun ranar litinin da ta gabata.

Sanarwar da ta bayana labarin , tace mafi yawan tashe tashe hankullan da aka samu, a cikin ayyukan ƙiddayar, sun faru a jihohin gabancin ƙasar, da su ka haɗa da Anambra, Abia,Aqua Ibon,Inugu da Imo.

Ya zuwa yanzu a ƙalla mutane 10, su ka rasa rayuka, a sakamkon rikicin da ya abku, a sanadiyar ƙiddayar. Mutane 82, da a halin yanzu, ke tsare a wurarare daban daban na ƙasa, an zarge su da hadasa gobara, ko tozarta jami´an ƙiddaya, da dai sauran ayyukan ashsha, da dabaibaiye ƙidayar, inji Haz Iwendi, kakakin yan sandar Nigeria.