1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya rincaɓe a ƙasar Guinee

Yahouza S. MadobiFebruary 13, 2007

Ƙungiyoyin fara hulla sun shiga kwana na 2, na yajin aiki a ƙasar Guinee

https://p.dw.com/p/BtwG

Ƙungiyoyin fara hulla da jama´iyun siyasa a ƙasar Guine, sun shiga kwana na 2, na yajin aikin sai illah masha Allahu da su ka fara jiya litinin.

A ranar farko ta wannan yajin aiki, kussan mutane 20 su ka rasa rayuka, a cikin arangama tare da jami´an tsaro.

Daga farko rikicin awatan Janiru da ya wuice yanzu baki daya mutane fiye da 100 su ka kwanta dama.

A saboda haka shugaba Lansana Konte ya kafa dokar ta ɓace a fadin ƙasar baki ɗaya.

A cikin wani ɗan taƙattacen jawabi da ya gabatar ta kafofin sadarwa, ya ce gwamnati ta hanna fita tsawan sa´o´i 20 a ko wace rana , sannan an haramta shirya tarruruka ko wane iri.

Bugu da kari ya ba jami´an tsaro umurni na kar su yi sabba, ga mutumen, kokuma duk gidan da su ke da zatto a na shirya makirci a ciki sa.

Sanarwar ta shugaban ƙasa ta saka takunkumi ga kafofin sadarwa.

Gabanin wannan jawabi, ƙungiyar gamayya turai, da tarayya Afrika, da ita kanta Majalisar Ɗinkin Dunia, sun nuna damuwa, a game da halin da Guine ta tsunduma a ciki.

Fadar mulkin ƙungiyar taraya Afrika ta yi kira da babbar murya ga shugaba Lansana Konte, ya naɗa saban Praministan ta hanyar tuntunɓar juna, da ɓangarori daban-daban.

Idan dai ba a manta sabon rikici ya barke a sakamakon nada Praminista da bai samu goyan bayan ba daga ƙungiyoyin ƙwadago, wanda su ke zargi da zama dan amshin shatan shugaban ƙasa.

Sakataran zartaswa na AU Alfa Omar Konare, ya bayyana buƙatar girka komiti mai zaman kansa, na ƙasa da ƙasa wanda zai biciken kissan gilar da ya wakana a ƙasar Guine.

Halin da ake ciki akasar ya shafi hatta da kafofin sadarwa, inda ranar jiya, sojoji su ka yi kaca.kaca da wani gidan rediwo mai zaman kann sa su ka kuma yi awan gabada ma aikata 2, sannan wasu karin rediyoyin 2 sundakatar da ayyukansu dalili da sunsamu kashedi da barazana.

Ta fannin zirga-zirga ma, ƙasar ta fara komawa saniyar ware, domin kampanoni da dama, da su ka haɗa Air France, Air Senegal, da Air Ivoire, sun dakatar da zirga zirgar jiragen su zuwa birnin Konakry.

Sannan rahottanin baya-bayan na nunar da cewa an fara samun bore daga ɓangaren sojoji, wanda da kan su ne, shugaba Jannar Lansana Konte ke dogaro.